Danwake da garin kuli

Yar Mama
Yar Mama @YarMama
Bauchi

Danwake da garin kuli

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

40mintuna
3 yawan abinchi
  1. Filawa gwangwani biyu
  2. Kuka cokali daya
  3. gwangwaniRuwan kanwa rabin
  4. Garin kuli
  5. Man kuli
  6. Dunkule
  7. Albasa

Umarnin dafa abinci

40mintuna
  1. 1

    Ki tankade gari filawa ki hada da kuka

  2. 2

    Ki zuba ruwan kanwa sai ki kwaba kar yayi karfi sosai.

  3. 3

    Ki daura ruwa a wuta idan ya tafasa sai ki fara gutsira kina jefawa cikin ruwan har ki gama sai ki rufeshi amma kar ki matsa a wajen.

  4. 4

    Idan ya tafasa zaiyi kokarin zuba sai ki bude ki dan sa abun gaurayawa.

  5. 5

    Idan ya tafasa na biyu sai ki kwashe. Ki zuba a ruwa mai sanyi.

  6. 6

    Ki soya man kuli da albasa

  7. 7

    Idan kika tsame danwaken kika zuba a plate sai ki barbada dunkule, kisa garin kuli sai kisa mai. Aci dadi lafiya.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Yar Mama
Yar Mama @YarMama
rannar
Bauchi
Kitchen is my favorite place
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes