Danwake

Nafisa Idaya(Ummu Nazifs Kitchen)
Nafisa Idaya(Ummu Nazifs Kitchen) @nafisaidaya

Mijinah na matukar son danwake sosai da sosai dan baiki kullum yaci danwake ba nikuma tun banaso harya koyamun cin danwake #danwakecontest

Danwake

Mijinah na matukar son danwake sosai da sosai dan baiki kullum yaci danwake ba nikuma tun banaso harya koyamun cin danwake #danwakecontest

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. 3Filawa Kofi
  2. Kanwa yar karama
  3. Kuka babban cokali 2
  4. Maggi
  5. yajin burkono
  6. Mangyada

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Dafarka zaki jika kanwarki a Kofi ki tankade fulawa a kwano ki saka kuka

  2. 2

    Ki kwaba waje daya yayi daidai kar yayi tauri sosai kuma kar yayi ruwa ki daura tukunya kisa ruwa issashe idan ya tafaso saiki fara jefa kullun a tukunyar iya girman da kikeso

  3. 3

    Saiki rufe tukunyar daya fara tafasowa saiki dauko mastami ko cokali kina gaurayawa sama sama kunfar na komawa harsai kunfar ta lafa toh danwake ya nuna saiki kwashi a ruwa mai tsafta

  4. 4

    Ki dauraye ta saikisa a kwano ko plate kisa kayan hadi maggi mangyada da burkono kina iya sa kwai ko salad

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Nafisa Idaya(Ummu Nazifs Kitchen)
rannar

sharhai

Similar Recipes