Gashin Tsiren En Gayu

Asmau Minjibir
Asmau Minjibir @Emjays_cuisines
Kano

Ban taba sanin dadin gashin Tsiren nan ba Sai da nayi wa abokan oga da sallah, sakamakon kayan lambu na Koren tattasai, da Jan tattasai, da albasa yasa na bashi suna tsiren En gayu. Wannan tsire Sai kin gwada er uwa. Godiya ga ayzah cuisine da cookpad da suka bamu wannan damar ta koyon irin wannan hadin na en gayu. *#NAMANSALLAH*

Gashin Tsiren En Gayu

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan

Ban taba sanin dadin gashin Tsiren nan ba Sai da nayi wa abokan oga da sallah, sakamakon kayan lambu na Koren tattasai, da Jan tattasai, da albasa yasa na bashi suna tsiren En gayu. Wannan tsire Sai kin gwada er uwa. Godiya ga ayzah cuisine da cookpad da suka bamu wannan damar ta koyon irin wannan hadin na en gayu. *#NAMANSALLAH*

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Naman/tsokar Rago (girman hannu)
  2. Albasa (madaidaiciya guda 1)
  3. Jan tattasai (manya guda 4)
  4. Koren tattasai(manya guda 4)
  5. Kuli kuli(Kofi 1)
  6. Dakakken barkono(kwatan Kofi)
  7. TafarnuwaDanya(guda 4)
  8. Mai(Rabin Kofi)
  9. Dandano dunkule(guda 2)
  10. Dandano onga (guda 1)
  11. Dakakkiyar citta(Rabin karamin cokali)
  12. Curry(karamin cokali 1)
  13. Dakakken masoro(rabinkaramin cokali)
  14. Dried thyme(karamin cokali 1)
  15. Tsinken tsire(guda 8)

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki samu zallar tsoka, ki wanke ta Sai ki yayyanka ta zuwa madaidaitan dunkule. Sai ki zuba a roba ki goga albasa da tafarnuwa a kai, masoro, citta, curry, thyme, dandano, barkono, kuli kuli, da Mai, saiki juya sosai ko Ina da ko Ina na naman, sannan ki rufe ki ajiye shi a furunji na tsawon awa 1 da rabi

  2. 2

    A gefe Kuma ki gyara albasarki da ja da Koren tattasai Sai ki yankasu manya manya. Sannan ki jika tsinken tsiren ki a ruwa saboda kada yayi saurin konewa

  3. 3

    Ki ciro hadaddun namanki, ki juye a kasko ki soya shi Sama Sama, Sai ki zuba ruwa kwata Kofi, ki rufe ki barshi ya dahu ruwan ya tsotse. Sai ki sauke ki barshi ya Sha iska

  4. 4

    Sai ki dauko tsinken tsiren ki ki fara jera nama, kore da Jan tattasai da albasa Har yadda zaikai Rabin tsinken, kiyita jerasu Har naman ya kare

  5. 5

    Sai ki kunna wutarki a abin gashin tsire, ki shafa wa tsinken namanki Mai, ki barbada mashi kuli kuli, Sai ki fasa shi. Shikenan tsiren En gayu ya hadu.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Asmau Minjibir
Asmau Minjibir @Emjays_cuisines
rannar
Kano

sharhai

Similar Recipes