Kunun Alkama

mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
Kaduna State, Nigeria

#KadunaState.Alkama wani nauin abinci neh da ke dauke da sinadarai kamar iron,thiamine, niacin,calcium da sauransu,da kuma sinadaran da suke taimakawa wajen narkar da abinci a jikin mutum.Yana da amfani sosai a jiki.

Kunun Alkama

#KadunaState.Alkama wani nauin abinci neh da ke dauke da sinadarai kamar iron,thiamine, niacin,calcium da sauransu,da kuma sinadaran da suke taimakawa wajen narkar da abinci a jikin mutum.Yana da amfani sosai a jiki.

Edit recipe
See report
Share
Share

Ingredients

  1. Garin alkama rabin kofi(kar yayi laushi sosai)
  2. Kofi 4 na ruwa
  3. Madarar gari rabin kofi
  4. Sikari daidai bukata
  5. Rabin karamin chokali na Garin Habbahan(cardamom)
  6. Dabino (dai dai bukata)
  7. Gyada soyayya (dai dai bukata)

Cooking Instructions

  1. 1

    Da farko zaki Samu tukunya ki juye ruwan a ciki seh ki zuba madara ki juya(kina iya amfani da madarar ruwa ta kwali).

  2. 2

    Sannan ki zuba garin alkamar a ciki ki juya sosai da whisk ya zama ba gudaji.seh ki dora akan wuta kina juyawa akai akai idan ya dan fara kauri seh ki zuba garin habbahan ki cigaba da juyawa har seh yayi kauri amma a kula kada ya tafaso ya zube.

  3. 3

    Idan yayi kauri seh ki sauke ki zuba sikari ko zuma seh ki babbala dabinonki ki zuba akai da gyada.kina iya saka duk abin da kike so ko gyadar almond, kashew ko kayan marmari kamar ayaba ko busashen inabi.

Edit recipe
See report
Share

Cooksnaps

Did you make this recipe? Share a picture of your creation!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
on
Kaduna State, Nigeria

Comments

Similar Recipes