Kayan aiki

  1. Alayyahu
  2. Wake
  3. Nama
  4. Kuli,kayan yaji
  5. Wake kadan
  6. Mañja,mai,ruwa
  7. Dandano amma ni nafi using star sometimes da ajino

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko Ina yanka alayyahu na in wanke tas in tsane shi

  2. 2

    Sai in yi jajjagen tarugu tumatur albasa tattasai in aje gefe

  3. 3

    In tafasa nama in aje da ruwan in yi kul-kulen kuli da wake kadan da tafarnuwa,citta,diyan miya da bakin yaji

  4. 4

    Sai in Dora mañja na da mai yayi zafi Sai in zuba jajjage in soya in ya soyu Sai in zuba kul-kule na in cigaba da soyawa

  5. 5

    In ya soyu Sai in zuba ruwan tafashe in basu isa ba in kara ruwa in zuba nama da dandano

  6. 6

    In ya dahu Sai in zuba alayyahu na

Yanayi

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan

Wanda aka rubuta daga

Maryam Sani
Maryam Sani @Maryamsfada
rannar
Ina son girke-girke musamman na kayan kwalam
Kara karantawa

Similar Recipes

More Recommended Recipes