Edit recipe
See report
Share
Share

Ingredients

Cooking Instructions

  1. 1

    Ki zuba ruwa a tukunya daidai yanda zai isa ki dan sa mai dai ki barshi ya tafasa in ya tafasa seki samu kwano daban ki zuba semolina dan daidai ki zuba ruwan sanyi ki juya se ki zuba cikin ruwan zafi kina juyawa a hankali(talge/rude)ki rufe tukunyar kibari ya dan tafasa(10mins) se ki zo kina zuba ragowan semolina a hankali kina tukawa har yay Laushi Se ki rufe shi yanda steam ba zai fita ki barshi yay steaming kaman na (10-12)mins in yayi se ki kwashe kina sawa a leda Santana kina kullewa.

  2. 2

    Ki samu namanki ki wanke tsaf, ki sa a tukunya da ruwa daidai yanda zai dafashi kisa jajjagen attarhu albasa da lawashi. Maggi da ginger da garlic kinbarshi har seya dahu se ki ajiye gefe.

  3. 3

    A tukunya daban kisa manja ki soya da gishiri kadan(yana rage after taste din manja)se ki kawo jajjagen attarhu da su albasa kisa ki sa daddawa ki soya sama sama se ki kawo ruwan nama ki da nama ki zuba ki saida ruwan miya (zaki iya kara maggi in baiji ba) ki kawo wake da kika dan farfasa ki zuba ki rufe ki barshi yay ta dahuwa har se waken yayi laushi (zakiji yana bada kamshin dadi😋)se ki kawo buseshiyar kubewarki me kyau kina zuba wa da kadan kadan kina kadawa har yay kaurin da kikeso.

Edit recipe
See report
Share
Cook Today
khayrees Tasty bites
khayrees Tasty bites @cook_14456829
on
#Jigawa
Dr 👩‍⚕️Good food loverGood food for good mood Is our slogan ❤️
Read more

Comments

Similar Recipes