Dambun naman rago

Habiba Abubakar
Habiba Abubakar @UmmuMuhammad2
Sokoto

Yana da sauki ga Dadi sann Kuma be da illa ga lafiya

Dambun naman rago

Yana da sauki ga Dadi sann Kuma be da illa ga lafiya

Edit recipe
See report
Share
Share

Ingredients

  1. Naman rago mara kitse
  2. Mangyada
  3. Kayan dandano
  4. Gishiri
  5. Tarugu
  6. Albasa
  7. Garlic

Cooking Instructions

  1. 1

    Zaki gyara naman ragonki ki sa cikin container domin Shi baa cika wankewa ba saboda Yana da ruwa a cikinshi

  2. 2

    Sai kisa kayan kamshi da na dandano da gishiri da albasa da tafarnuwanki da tarugu a cikin naman Sai ki juya Shi sosai ki rufe ya Sami awoyi saboda kayan hadin ya shiga cukin naman sosai.zama kiga ya tsatso ruwa da kanshi

  3. 3

    Sann ki juye cikin tukunya ki daura a wuta ki barshi ya dahu sosai Sai ki sauke ki Sami turmi ki zuba a ciki ki daka Shi ya daku sosai.in ya daku zakiga ya Zama Kamar soso

  4. 4

    Sai ki kwashe ki sa shi tray ya Sha iska.

  5. 5

    Bayan namanki ya Sha iska Sai ki sa abin suya a wuta ki diga mangyada a ciki kadan Sai ki zuba naman a ciki kina juyawa a hankali har Sai ya Zama golden brown to ya soyu kenan Sai ki sauke

  6. 6

    In dambun nanki ya Sha iska Sai ki Sami abin kankare kubewa Sai ki dinga diban dambun kin gogawa Kamar yanda like goge kubewa.zakiga dambunki ya Zama Kamar auduga.

  7. 7

    Zaki iya ci haka nan ko da lemu

  8. 8

    A ci lafiya

Edit recipe
See report
Share
Cook Today
Habiba Abubakar
Habiba Abubakar @UmmuMuhammad2
on
Sokoto
cooking is full of fun
Read more

Comments

Similar Recipes