DOYA MAI KWAI

Bint Ahmad
Bint Ahmad @Bint92
Sallari,Kano Nigeria.

#PAKNIG...RAMADAN MUBARAK..Allah ubangiji ya karbi ibadunmu,Ya jikan magabatamu.

DOYA MAI KWAI

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan

#PAKNIG...RAMADAN MUBARAK..Allah ubangiji ya karbi ibadunmu,Ya jikan magabatamu.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

45mintuna
2 yawan abinchi
  1. Rabin karama Doya
  2. 8Kwai
  3. Albasa karama
  4. Gishiri da Maggi
  5. Man Suya
  6. Ruwa
  7. Sugar (optional)
  8. 2Attarugu

Umarnin dafa abinci

45mintuna
  1. 1

    Zaki fere doya ki wanke,ki zuba a cikin tukunya kisa ruwa,gishiri,da sugar amma sugar bai zama dole asa ba ki juya ki rufe abar ta ta dahu sosai tayi laushi.

  2. 2

    Zaki zuba mai a kaskon suya ki zuba ‘yar albasa Don yayi kamshi wajen suya kafin yayi zafi,a gefe ki sami kwano mai zurfi ki fasa kwai kisa albasa da jajjagen attaruhu ki kada,gefe guda kin tsame doyar ta huce sai ki yanka yanda kike so.

  3. 3

    Idan mai yayi zafi sai kina tsoma doya a ruwan kwai ki juya ta a ciki sai ki dako ki saka a manki mai zafi ki soya har su soyu.Kinayi ki juya daya barin idan kika ga yayi maki suyar da kike so sai ki tsame ki zuba a mazubi mai kyau da tsabta.Musha Ruwa Lafiya

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Bint Ahmad
Bint Ahmad @Bint92
rannar
Sallari,Kano Nigeria.
For me,the kitchen is the most special room in the house.Its a place for adventure -not drudgrey,but discovery,sharing and showing off with friend's,trying new ideas.♡☆
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes