Kayan aiki

  1. Gyada
  2. Nikakken Kayan miya
  3. Tafashen nama
  4. Albasa
  5. Alayyahu
  6. Manja
  7. Hadin daddawa
  8. Tafarnuwa/ginger
  9. Kabushi
  10. Kayan dandano

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ki gyara kabushi ki wanke, sai Kisa a tukunya ki zuba ruwa kibarshi ya tafasa. Ki zuba mai a tukunya sai ki yanka albasa in ta fara soyuwa sai ki sa tafarnuwa da ginger, ki zuba Nikakken Kayan miya da nama.

  2. 2

    Ki zuba daddawa. kabushin zaki nika/daka shi idan kayan miyan ya soyu sai ki zuba.

  3. 3

    Kisa ruwa ki zuba sinadaran dandano ki rufe ta dahu na minti 10. Alayyahu ki gyara ki wanke bayan 10m sai ki zuba ki sake rufewa

  4. 4

    Ki murza gyaɗa ki cire bayan sai ki nikata.

  5. 5

    Sai ki zuba gyadar idan kika ji kanshin gyadar alamun miyar tayi sai ki sauke.

  6. 6

    Aci da tuwo ko masa😋🤤

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Ummu_Zara
Ummu_Zara @ummu_zaraskitchen
rannar
Sokoto State
sunana Rukayya Ashir saniIna son yin girki kala-kala, Abubuwa da yawa dangane da kitchen suna burgeni.
Kara karantawa

Similar Recipes