Yadda zaki adana Tattasai, Shambo da Attarugu

Jamila Ibrahim Tunau
Jamila Ibrahim Tunau @Jamitunau
Sokoto State

Idan kin gwada wannan zakiki ji dadin shi sosai. Lokacinda yake tsada.

Yadda zaki adana Tattasai, Shambo da Attarugu

Masu dafa abinci 14 suna shirin yin wannan

Idan kin gwada wannan zakiki ji dadin shi sosai. Lokacinda yake tsada.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Tattasai buhu 3 100kg kowane
  2. Shambo buhu 2 50kg kowane
  3. Attarugu buhu 1 50kg
  4. Wannan lissafi nayi shi ne tsakanin watan January da ka sawo
  5. 2020Zuwa watan February na shekarar

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ana sayar da buhun tattasai akan naira dubu 6 100kg wanda zaki sa acire miki hancin da diyan akan dari 700, karamin buhu kuma solo akan 500

  2. 2

    Tattasai shine me kiba da dan tsawo shikuma shambo siriri ne da dan tsawo shikuma tarugu ko attarugu gajere ne kuma baya da girma

  3. 3

    Shi kuma shambo ana sayar dashi akan dubu 2 da dari 500 kowane buhun solo 50kg shima zaki sa acire hancin a yanka shi 2 akan 500 kowanne buhu

  4. 4

    Shi kuma attarugu yana kaiwa dubu 9 karamin buhu solo wasu kuma dubu 8 hakanan zaki shanya shi wasu na sayen slippers sabbabi se ayita takawa amma ni ahaka muke shanya wa.

  5. 5

    Idan an cire zaki iya shanyawa a siminti ko kuma asawo miki leda akan dari 800 se ki baza baa juyawa dole ne ki kyaleshi yadda yake Do not disturb.

  6. 6

    Yana daukar kusan sati 2 kafin ya bushe kuma baa shanyawa cikin inuwa baki yakeyi zaki bar shi ne cikin rana

  7. 7

    Idan ya bushe zaki zube aroba kidan karkada shi sauran ragowar diyan ya cire se ki kulla tattasai kwano 4 ledar purewater ke dauka shi kuma shambo kwano 3

  8. 8

    Seki adana wurin da babu sanyin ruwa wannan zeyi miki kusan wata 4 zuwa 5 kina morewa wasu ma yakan fi hakan

  9. 9

    Shide tattasai idan ya bushe lokacin da zeyi tsada zaki jika shi ne da ruwan pampo dadare da safe zakiga yafito kaman danye ko kuma tunda safe idan zakiyi miyar rana se ki saka albasa da tarugu da kabewa a nika miki tare miyarki ta hadu saboda ni bana son busashen tumatur yana sa miya tayi baki ko duhu. zaki iya kuma cire kabewar a nika hakanan se kisaka tumatur na gwangwani

  10. 10

    Shikuma shambo muna amfani da shi cikin kosai ko alala shima zaki jika da safe kafin ki wanke waken ki yayi laushi se aniko miki shi tare ba kaman tattasai ba shi kosan ki beze sha mai ba kuma zeyi kyau ga dadi idan kin hada da tarugu kadan zaki iya amfani dashi kuma wurin yin jollof rice wannan kam baa magana hade idan ga lawashi aciki

  11. 11

    Se na karshe shine lawashi shima zaki yanka shi kanana se ki wank kisaka a rariya ya tsane ruwan shi se ki kulla a leda kisa a freezer dede wanda ze isheki na miyar ganye ko kuma cikin jollof wasu kuma suna yankawa su shanya ya bushe amma shi acikin inuwa zaki shanya shima kisamu leda ki kulla ko kuma adaka ana sawa wurin tafasar nama ko kaza yana rage mata karnin nan

  12. 12

    Racikin duk buhu 1 na shambo zaki samu kusan kwano 9 shikuma tattatsai kusan kwano 20 ko fiye

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Jamila Ibrahim Tunau
rannar
Sokoto State
The kitchen is my comfort zone.
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes