Tuwo miyar taushe

Fatima's Kitchen
Fatima's Kitchen @cook_16962986

Wannan miya itace miyar taushe miyarmu ta hausawa tayi dadi sosai😋😋

Tuwo miyar taushe

Wannan miya itace miyar taushe miyarmu ta hausawa tayi dadi sosai😋😋

Edit recipe
See report
Share
Share

Ingredients

  1. Kabewa
  2. Maggi
  3. Oil
  4. Tattasai
  5. Attarugu
  6. Albasa tumatir
  7. Gyada
  8. Gishiri kadan
  9. Alayahu
  10. Kaza

Cooking Instructions

  1. 1

    Da farko zaki hada tattasanki da attaru albasa tumatir ki nikasu

  2. 2

    Sai ki kawo kabewar ki ki fere ta ki wanke ta ki zuba ruwa a kisa tukunya saiki dafata idan ta dafu sai ki sauke ki tsaneta ki daka ta a turmi ki ajiyeta a gefe

  3. 3

    Ki kawo tukunyaki ki tsuba oil a ciki kisa albasa ki sa kazar ki Wanda kika Riga kika tafasa ki soya ta a oil ta soyu idan ta soyu saiki ajiyeta gefe

  4. 4

    Ki kawo kayan miyan da ki ka markada sai ki zuba a cikin mai ki soya ta sai ki kawo kabewar ki da kika dafa ki sa ka ki soyasu idan suka soyu saiki zuba ruwa Bada yawa ba kisa maggi da gishiri kada saiki sa gyadarki ki rufeta

  5. 5

    Ki barta ta yi idan tayi sai ki dakko kazarki ki saka ki sa alyahun ki da kika Riga kika gyara aciki ki cuya sosai sai ki rufeta ta karasa dahuwa

  6. 6

    😋😋😋

Edit recipe
See report
Share

Cooksnaps

Did you make this recipe? Share a picture of your creation!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Fatima's Kitchen
Fatima's Kitchen @cook_16962986
on

Comments

Similar Recipes