Burodin alkama mai kwakwa

Salwise's Kitchen
Salwise's Kitchen @cook_16516066
Zaria

#BAKEBREAD wannan sabon hanyar yin burodi ne,Wanda na had'a da kaina,wato da alkama,ganin yadda na fulawa yayi yawa,a gaskiya yayi dad'i sosai da gardi.

Burodin alkama mai kwakwa

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin

#BAKEBREAD wannan sabon hanyar yin burodi ne,Wanda na had'a da kaina,wato da alkama,ganin yadda na fulawa yayi yawa,a gaskiya yayi dad'i sosai da gardi.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Awa daya da mitoci
Uku
  1. Garin alkama gwangwani uku
  2. Sikari cokali uku
  3. cokaliYeast karamin
  4. Madara cokali biyar
  5. Bota cokali uku
  6. Gurzajjiyar kwakwa cokali biyu

Umarnin dafa abinci

Awa daya da mitoci
  1. 1

    Ga kayan hadin mu,kamar haka,za'a gyara alkamar tsaf,sannan anika ya zama gari,a tankad'e.

  2. 2

    Za'a jika yeast din da ruwan dumi,a ajiye 6arayi guda har ya kumburo kamar haka

  3. 3

    Sai zuba bota,sannan a zuba garin madarar,sannan a zuba yeast da sikarin da aka jika,kamar haka

  4. 4

    Sai a jujjuya su hade,kamar haka,sannan a rufe a ajiye awaje mai dumi,abarshi yayi awa days,gashi nan za'a ga ya tashi

  5. 5

    Sai a barbada garin alkamar a faranti silba a jujjuya na tsahon minti biyar

  6. 6

    Sai a mulmula kamar haka a barbada kwakwa,sannan a shafa bota a kwanon silbar,a barbada garin alkamar sannan a saka burodin,sai a gasa,kamar yadda za'a gani,nayi amfani da yashi ne(local baking)

  7. 7

    Ga burodin mu ya gasu

  8. 8
Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Salwise's Kitchen
Salwise's Kitchen @cook_16516066
rannar
Zaria
I was born and bred up in Zaria
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes