Alkubus na alkama

mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
Kaduna State, Nigeria

#KadunaState.Alkubus yana daga cikin abincin gargajiya da ake yin shi da garin alkama ko fulawa,ana cin shi da miyar taushe ko kabewa ko farfesu da sauransu.

Alkubus na alkama

Masu dafa abinci 9 suna shirin yin wannan

#KadunaState.Alkubus yana daga cikin abincin gargajiya da ake yin shi da garin alkama ko fulawa,ana cin shi da miyar taushe ko kabewa ko farfesu da sauransu.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Kofi 2 na garin alkama
  2. Yeast babban chokali 1
  3. Gishiri karamin chokali 1
  4. Ruwan dumi yadda ake bukata
  5. Mai

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki samu garin alkama ki zuba a roba meh zurfi seh ki zuba yeast,mai babban chokali 2 da gishiri a kai ki juya.

  2. 2

    Seh ki rika zuba ruwan dumi kadan kadan ki kwaba da muciya ko hannu bayan kin wanke har seh ya hade amma kada yayi ruwa tsululu kuma kada yayi tauri,ki buga shi sosai seh ki sami kling film ki rufe ki sa waje meh dumi ya tashi.

  3. 3

    Bayan ya tashi seh ki sake buga shi,seh ki shafa mai a cikin mazubin da zaki zuba ki dibi kullun ki zuzzuba a ciki amma kar ki cika saboda zeh kara tashi seh ki jera cikin steamer ki rufe da buhu kar tiririn ya rika fita,ki zuba ruwan dumi cikin kasan steamer din ki dora kan wuta,idan ruwan na kara zafi zeh sa ya kara tashi kafin ya fara turaruwa.

  4. 4

    Idan ya turaru zaki ji kamshi ya cika Koina ko ki sa wuka ciki idan ta fito ba kullin a jiki alkubus dinki ya turaru.seh ki sauke, a ci da miyar taushe meh kabewa ko farfesu.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
rannar
Kaduna State, Nigeria

sharhai

Similar Recipes