Gasashen Nama (Gashin kasko ba oven)

Jahun's Delicacies
Jahun's Delicacies @4321ss
Kano,Danladi Nasidi Estate.

#NAMANSALLAH Wanan gashi ba kamar kowanne gashi bane,yana da dandano mai gamsarwa, sanan yana da laushi saboda ana dafa shi kafin a gasa,sanan wanan hadi da akayi masa yasa gashin ya kayatar da mai ci.

Read more
Edit recipe
See report
Share

Ingredients

  1. Nama
  2. Tsokar nama guda 2 masu nawin giram dari shida da sittin
  3. Kayan hadi(tsimin nama)
  4. cokali Hadin kori-rabin karamin
  5. Dakakkiyar citta-karamin cokali daya
  6. cokali Cumin seed dakakke-rabin karamin
  7. cokali Masoro dakakke-rabin karamin
  8. cokali Rosemary dakakke-rabin karamin
  9. Gishiri -karamin cokali daya
  10. Maggi-guda uku
  11. Mai-daya bisa hudu na kofi
  12. Barkono dakakke-babban cokali daya
  13. Hadin mayonnaise
  14. Kwai-daya
  15. cokali Gishiri-rabin karamin
  16. cokali Kori-rabin karamin
  17. Siga-karamin cokali daya
  18. cokali Citta dakakkiya-rabin karamin
  19. cokali Barkono-rabin karamin
  20. cokali Ruwan leman tsami-rabin karamin
  21. Mai-daya bisa uku na kofi
  22. Dahuwa da gashi
  23. Ruwa-kofi uku ko fiye da haka
  24. Bota-babban cokali biyu
  25. 'Ya'yan koriander
  26. Kayan aiki
  27. Leda
  28. Kaskon suya
  29. cokali Babban
  30. Wuka

Cooking Instructions

  1. 1

    Zaki samu roba ki zuba dukkan kayan kamshin dana lissafa na tsimin nama tare da maggi da gishi ki juya.

  2. 2

    Wanan itace ledar da nayi amfani da ita wajan tsima naman.

  3. 3

    Zaki samu nama mai kyau babu kashi babu kitse babu jijiya, zaki saka a leda ki zuba wanan hadin kayan kamshin.

  4. 4

    Sanan ki zuba mai ki murtsuka sai ki ajiye a fridge tsawon awa daya dan ya tsimu, amma ba dole bane, sai dai duk naman da aka tsima yafi dadin dandano.

  5. 5

    Zaki dauko shi daga fridge ki saka a kaskon suya,daga nan sai ki zuba ruwa ki rufe har sai ya dahu,zaki ringa soka wuka dan ki tabbatar da laushin sa. Amma ba'a so ruwan yayi yawa dan zakin naman bazai kama jikin naman ba, ga yanda ake so yayi. Wato ruwan dahuwar ya qafe a jikinsa.

  6. 6

    Zaki dauko wani kaskon suyar ki saka bota a ciki.

  7. 7

    Da 'ya'yan coriander ki kunna wuta.

  8. 8

    Idan botan ya narke sai ki saka naman ki ki soya dukkan bangaren.

  9. 9

    Ga yanda namanki zai kasance bayan kin gama suyar.

  10. 10

    Sai hadin mayonnaise,zaki fasa kwai a roba ki zuba ragowar kayan hadin dana lissafa nayin mayonnaise amma banda mai.

  11. 11

    Kamar haka.

  12. 12

    Zaki juye a blanda ki markada tsawon minti biyar, sai ki tsaya ki zuba mai, kina markadawa kina tsiyaya man zakiga yana kauri.Bayan kin gama sai ki zuba a kwano ko roba karama. Shi wanan mayonnaise da shi za'a ci wanan nama.

  13. 13

    Toh gashin nama da mayonnaise ya hadu.

  14. 14

    Ga yanda cikin naman yake, shi yasa yake da mahimmanci a bashi lokaci ya dahu.

  15. 15

    Zaki ci wanan gasashen nama da hadin mayonnaise da kika yi, dadi dai ba'a magana.

  16. 16

    Ga abin awo danake amfani dashi a kitchen.

Reactions

Edit recipe
See report
Share

Comments

Written by

Jahun's Delicacies
on
Kano,Danladi Nasidi Estate.
Sadiya Salisu Jahun,was born and brought up in kano,an Msc.holder on Agricultural Extension,i love cooking and i think to be a great chef you have to be a great teacher, i love doing classes with people who loves and enjoy food,bringing them all around one table to speak.
Read more

Similar Recipes