Faten tsaki da rama

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan
Mufeeda
Mufeeda @cook_17361783
Kaduna

#MLD
Faten tsaki wani abincine da akeyi a arewacin Nigeria, musamman yankin Zaria, Wanda ake yi da tsakin masara ko na shinkafa.

Kara karantawa
Gyara girkin
See report
Tura

Kayan aiki

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Idan da nama za a yi ko tantakwashi, sai a wanke a yanka albasa, a sa gishiri da sinadarin dandano a tafasa.

  2. 2

    Bayan tafasa nama, sai a tsaida ruwa daidai gwargwado, a sa markadadden tattasai, tarugu, da albasa. Sai a sa sinadarin dandano, da gishiri, sai a rufe a bar Shi ya tafasa.

  3. 3

    Idan ruwan ya tafasa sai a wanke tsaki a rege, sai a zuba tsakin a ciki a juya. Sai a farfasa gyada a bakace, a zuba cikin tsakin, a na juyawa lokaci zuwa lokaci dan Kar ya dunkule wuri daya a kasa.

  4. 4

    Idan tsakin ya dahu, sai a zuba manja, a juya, sannan sai a wanke rama, a yanka ta da dan girma, sai a zuba a cikin dahuwan, a barshi yayi minti 5 zuwa 10 saboda rama na da dan tauri ba kaman alayyahu ba. Sai a sauke a zuba a paranti. A na iya sa kakidi ko man shanu yayin sha.

Yanayi

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan

sharhai

Wanda aka rubuta daga

Mufeeda
Mufeeda @cook_17361783
rannar
Kaduna

Similar Recipes

More Recommended Recipes