My homemade burger

Hannatu Nura Gwadabe
Hannatu Nura Gwadabe @cook_18667831
Kano State

Burger akwai dadi sosai nayi mana nida maigidana km ya yaba sosai km yana qosarwa in kaci daya ma ya isheka.

My homemade burger

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin

Burger akwai dadi sosai nayi mana nida maigidana km ya yaba sosai km yana qosarwa in kaci daya ma ya isheka.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Burger bread
  2. Kaza (tsoka zalla)
  3. Albasa,
  4. attaruhu,
  5. salad,
  6. tumatir,
  7. sweet peppe,
  8. cucumber,
  9. tafarnuwa
  10. Seasoning,
  11. kayan qamshi
  12. Mayonnaise/kechup
  13. Flour
  14. Corn Flour
  15. Kwai
  16. Mai

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ki samu tsokar kaza ki yanka ta yanka mai fadi bamai tudu sosai ba saiki sa kayan qamshi ki jajjaga attaruhu,albasa da tafarnuwa ki zuba akan kazar saiki sa maggi da curry ki cakuda komai yabi jikin kazar sai ki marinating nata for 30 minutes atlest (maana ta tsumu)

  2. 2

    In kazar ki ta tsumu sai ki dora mai a wuta saiki fasa kwai a bowl yy zafi sai ki dinga daukan tsokar ki tsoma acikin ruwan kwai sai ki sa ta cikin flour sannan km kisa cikin corn flour sai ki soya shi har sai yy golden brown in yy crispy sai ki kwashe zai zama kamar KFC chicken

  3. 3

    Sai ki dakko bread enki ki yanka shi biyu part en sama yafi yawa sai dan dora shi acikin fan yadan gasu basai kinsa mai ba dama lokacin kin riga kin juye man da kk suya dashi to kinga zai zama pan en da maiqo a jiki to wannan ya isheki in yadan gasu saiki kwashe shi

  4. 4

    Saiki dauko bread enki qasan da kika yanka ki shafa mayonnaise/cream salad/ketchup duk dai abinda kk so wasu suna mayi ba ko daya ciki saiki dora wannan kazar da kika soya sannan ki dora salad enki basai kin yanya sannan kisa sa cumber da sweet peppe da tumatir amma ki yanka su in circle saiki dora saman bread enki.

  5. 5

    Ana iya ci da lemo ko kuma shayi,

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Hannatu Nura Gwadabe
Hannatu Nura Gwadabe @cook_18667831
rannar
Kano State
cooking is my hobby
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes