Shinkafa da Taliya

 B.Y Testynhealthy
B.Y Testynhealthy @B66579858
Kaduna

Wannan girki nayishine saboda farin cikin cika shekaru 59 da kasata Nigeria takeyi da samun ya'nci #oct1st

Shinkafa da Taliya

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan

Wannan girki nayishine saboda farin cikin cika shekaru 59 da kasata Nigeria takeyi da samun ya'nci #oct1st

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

30 minutes
3 yawan abinchi
  1. Kofi 2 Shinkafa
  2. 1/4Taliya
  3. Koren kalla na abinci yanda kalar zai fito (green food color)
  4. Marikin tuta
  5. Cinyar kaza
  6. 2Tattasai
  7. 3Attaruhu
  8. 1Albasa
  9. Mai
  10. Kayan kamshi
  11. 3Mai dandano

Umarnin dafa abinci

30 minutes
  1. 1

    Ki tafasa ruwa ki wanke shinkafa ki zuba, inta kusa dahuwa sai ki sauke ki dauraye ruwan da kika tafasa dashi ki tsane a abin tacewa

  2. 2

    Sai ki mayar tukunya ki kara ruwa kadan ki rufe ya turara, in yayi laushi ya kuma tsotse saiki sauke

  3. 3

    Taliya itama za a tafasa ruwa sai a karya biyu a zuba, sai a zuba kalar kore na abinci a barta ta dahu

  4. 4

    In kalar batayi kore sosai ba sai a kara yanda zai fito kalar tutar Nigeria sosai

  5. 5

    A tafasa cinyar kaza da albasa da kayan kamshi da mai dan dano, sai a soya a mai

  6. 6

    A jajjaga tattasai da attaruhu da albasa soya sama sama, a zuba ruwan tafasan kaza tare da kazar a dan kara mai dandano

  7. 7

    Sai a sami faranti a jera koriyar taliya a gefe farar shinkafa a kusa da taliya sai wata taliya a kusa da shinkafa, ya bada da kalar tutar Nigeria kenan, sai ayi marikin tuta da cinyar kaza. Aci da jar miya

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
 B.Y Testynhealthy
rannar
Kaduna

sharhai

Similar Recipes