Taliyar zogala

Ummi Tee
Ummi Tee @Ummitunau
Sokoto

#taliya tana cikin abinchi dakeda saukin dafawa akoda yaushi wannan dahuwar de, saka mata zogala a ciki ya kara mata inganchi wurin gina jiki.

Kara karantawa
Gyara girkin
See report
Tura

Kayan aiki

  1. Taliya daya
  2. Tattasai hudu,yankakke
  3. Albasa daya, yankakka
  4. Maggi goma
  5. 1Curry gino sashet
  6. 1/2 tspKayan kanshi,
  7. Tarugu biyu yankakke
  8. Maggi fari½tsp
  9. Gishiri Dan dandano
  10. Nikakken Tarugu da tattasai
  11. Mai, rabin kofi
  12. Yankakken lawashi
  13. Yankakken alayyahu
  14. Zogala kadan,agyara
  15. Ruwa yawan yadda kike son taliyarki

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Sinadiran hada wannan taliyar ta zogale

  2. 2

    Zaki dauko manki ki zuba cikin tukunya idan yayi zafi seki dauko tarugu tattasai da albasa ki zuba. Kinayi kina juyawa har ya soyu.

  3. 3

    Cikin wata tukunya daban ki zuba nikakkun kayan miya ki soya ya soyu idan sun soyu seki dauko su ki juye cikin dayar tukunyar ki motse su

  4. 4

    Se kidauko magi, farin maggi, curry,kayan kanshi se kizuba cikin suyarki kamar yadda kika gani a hoto ki soyasu tare su soyu

  5. 5

    Sai ki dauko ruwanki ki zuba yawan yadda kike so,(wasu nasonta da ruwa wasu nasonta tsane) ki zuba lawashinki da zogala ki rufe tukunya na dan tsawon lokachi

  6. 6

    Se kidauko taliyarki ki karyata kizuba ciki. ki motsa dan kada ta damke wuri daya se ki dauko marfi ki rufe

  7. 7

    Idan ta kusan tsanewa se ki zuba alayyahun ki da albasa ki rufe ta gama sulala

  8. 8

    Shike nan yaliyarki ta gama haduwa se ci hmm ba aba yaro me Kyuya😀

Yanayi

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan

Wanda aka rubuta daga

Ummi Tee
Ummi Tee @Ummitunau
rannar
Sokoto

Similar Recipes