Dafadukan taliya da macaroni

Safiyya Yusuf
Safiyya Yusuf @samgz2703
Sokoto

Dafadukan taliya da macaroni

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. 1Taliya sachet
  2. 1Macaroni sachet
  3. Tattasai
  4. Tarugu
  5. Albasa
  6. Tumatur
  7. Cabbage
  8. Naman rago
  9. Maggi
  10. Gishiri
  11. Mai
  12. Curry

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki fara tafasa namanki da maggi, gishiri da albasa

  2. 2

    Sai ki gyara kayan miyan ki ki jajjagasu gabadaya ki rufe gefe

  3. 3

    Saiki soya tafasasshen namanki bayan ya soyu saiki kwashe ki rage Mai sannan ki soya jajjagenki ciki.Bayan ya soyu saiki zuba ruwa dai-dai yadda zai isheki sannan ki zuba namanda Ki zuba ruwan tafashe sannan ki qara ruwa kisa maggi sannan ki dandana idan gishiri bai jiyaba sai ki qara kisa Curry ki rufe har ya tafasa

  4. 4

    Saiki dauko cabbage ki yanka ki wanki da Gishiri ki tsiyaye ki rufe

  5. 5

    Bayan ruwan sun tafasa saiki zuba macaroni saboda tadanfi taliya wuyan dahuwa Zaki bata 7mins sannan ki zuba taliya ki matsa saboda kada ta game wuri daya sannan ki rufe

  6. 6

    Idan ta nuna saiki zuba cabbage ki rage wuta sosai domin ya Dan dahu

  7. 7

    Bayan cabbage ya nuna saiki sauke.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Safiyya Yusuf
Safiyya Yusuf @samgz2703
rannar
Sokoto

sharhai

Similar Recipes