Gurasa

Masu dafa abinci 2 suna shirin yin wannan
mmn Khaleel's kitchen
mmn Khaleel's kitchen @cook_19001811
Jigawa State

Abinci ne na gargajiya mai dadin dandano😜😂

Kara karantawa
Gyara girkin
See report
Tura

Kayan aiki

  1. Filawa
  2. Yeast, gishiri,
  3. Hadaddan yajin qarago
  4. Albasa,tunatur,karas

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Yadda zaki kwaba bayan kin tankade fulawa Sai kisa yist da gishiri kadan ki juya Sai kisa ruwa kadan kifara kwaba shi kwabin yay kamar na alkubus wato karya yi ruwa kuma kar yay tauri yafi dai na fanke tauri bayan kin gama Sai kisa a rana ko wuri mai dumi Dan ya tashi

  2. 2

    Da zarar ya fara tashi to Sai ki kunna murhun gawayin ki ya fara ruruwa Sai ki Dora pan din ki saidauko Wannan kulun ki fara gashi yadda zaki gasa hanya biyu ne idan a pan zaki gasa bayan kin Dora shi ya fara daukan dumi Sai kisa hannun ki a ruwa Sai kuma ki Ciro fulawar kamar rabim hannun ki sa a pan din kidan buda shi kadan ki bari yayi minti 1zuwa 2 Sai ki juya bayan haka zaki tayi harya gasu

  3. 3

    Bayan kin gama Sai ki Ke saka shi a kula Dan yay laushi Sannan idan kk tashi amfani da ita Sai ki Dan tsomashi a ruwa ki Sauri ki cire Dan karya jike da yawa Sai ki hada abinki da yajin kuli da mangyada da su albasa abinki aci dadi lfy 😜😂🙋

Yanayi

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan

sharhai

Wanda aka rubuta daga

mmn Khaleel's kitchen
mmn Khaleel's kitchen @cook_19001811
rannar
Jigawa State
ina da son dafa abubuwa masu matuqar. dadi da birgewa
Kara karantawa

Similar Recipes

More Recommended Recipes