Sinasir din shinkafa

TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA) @cook_15480513
Port Harcourt

Sinasir abincine na gargajiya musamman akasarmu na borno muna sonshi sosai kuma yanada daraja sosai awurinmu

Kara karantawa
Gyara girkin
See report
Tura

Kayan aiki

  1. Chinkafar tuwo kofi shida
  2. Fulawa kofi day da rabi
  3. Suga rabin kofi
  4. chokaliGishiri rabin
  5. Baking powder rabin chokalin shayi
  6. Yeast chokali daya da rabi

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Dafarko zakidiba shinkafarki kugyara sai kiwanke kicire kasa aciki sannan kidiba kofi biyu kidafa bayan kindafa sai kizuba a tire kibarta tahuce

  2. 2

    Bayan tahuce sai kidauka kizuba akan wanda kika jika sai ki gauraya

  3. 3

    Bayan ki hadasu sai ki kai amarkada miki sannan kizo kitankade flour kofi daya da rabi kizuba aciki ko kofi biyu idan yayi ruwa sosai sai ki jujjuya sosai yanda flour zai narke duka aciki sannan sai kizuba yeast

  4. 4

    Bayan kinzuba yeast kisake juyawa sannan kizuba sugar rabin kofi da baking powder rabin chokali da gishiri dan kadan kisake jujjuyawa sai kirufe ki ajiye a wuri mai dumi zuwa awa daya ko daya da rabi don yatashi

  5. 5

    Gashinan bayan yatashi

  6. 6

    Sai kidaura nonstick pan a wuta idan yayi zafi sai kirage wutan sosai sannan kizuba mai kamar chokali daya aciki sai kizuba kullin aciki kamar ludayi biyu sannan kisamo murfin tukunya kirufe kibarta har yasoyu sai kicire kisake zuba mai sannan kizuba kullin. Haka zakiyi tayi har kigama

  7. 7

    Note....idan kinaso kiga wannan buli bulin da yasaka yayi manya manya sosai toh bayan kinhada dafaffen shinkafar da wanda kika jikan sai kidiba wake kamar rabin chokali kiwanke kicire bayan sannan kizuba akai sai kihada kimarkadasu tare sannan kizuba sauran hadin kibarta yatashi sai kisoya. Zakiga bulin yayi manya manya yafi wannan kyau

Yanayi

Gyara girkin
See report
Tura

sharhai

Wanda aka rubuta daga

TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
rannar
Port Harcourt
Gskiya arayuwata inason girki sosai shiyasa kullum ina kicin wurin tsara abinci kalakala
Kara karantawa

Similar Recipes