Miyan Ganda da Kaza da shinkafa fara

Jauhar Mukhtar Yusuf^jcuisine
Jauhar Mukhtar Yusuf^jcuisine @cook_21399775

Wannan girki yana da dadi sosai amma yanason Nutsuwa don familynka suji dadin ci

Miyan Ganda da Kaza da shinkafa fara

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin

Wannan girki yana da dadi sosai amma yanason Nutsuwa don familynka suji dadin ci

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

3hrs
shinkafa gongon
  1. Ganda
  2. Attaruhu
  3. Albasa
  4. Tomatos
  5. Tattasai
  6. Mai
  7. Maggi
  8. Kaninfari
  9. Citta
  10. Sinamon
  11. Tafarnuwa
  12. Kaza
  13. With Rise
  14. Shinkafa
  15. Carrot
  16. Pis
  17. Gishiri

Umarnin dafa abinci

3hrs
  1. 1

    Bayan na jika ganda ta jiku sai nawanketa sosai duk bakin jiki yafita, cikin tama nawankeshi na cire yadin ciki tayi fes

  2. 2

    Sannan nayankata madaidaici nasa a tukunya nadora saman wuta, nadauko cokali ma yatsu nasa domin yataimakamin wajan saurin yin laushin ganda

  3. 3

    Nabarshi yata dahuwa tsahon lokaci har ruwan ya kusa tsotse dama nasa mata ruwa wadatacce, naduba naga tayi laushi bawai laushi over ba dai-dai saina sauke na kwara mata ruwan sanyi nawanke ta kamar sau uku da ruwa sai natsaneta a kwalanda na aje gefe

  4. 4

    Na hada kayan miyana na gyara na wankesu nayi blanding dinsu tishi 1 kar yayi laushi sosai Inada albasa wada tacce sai na raba biyu nasa rabi a markade rabi nayankata slice na aje gefe Kayan kamshina na dakasu duka na aje gefe Dama kazana na dafashi nasoyata na aje gefe

  5. 5

    Nazuba mai a tukunya nasa albasa da dan yawa kafin tayi ja nazuba markadena nasa maggi sai na rufe zuwa wani lokaci naduba naga ta dahu har ruwan ya kusa shanyewa ta dauko hanyan soyuwa Ina juyata har ta hade jikinta sannan nadauko ganda nazuba tare da soyayyen kaza nadauko albasa na dana yanka tare da attaruhu guda 3 da na dan jajjaga inkinason yadanyi yaji sai kisa in bakyaso shikenan Nadauko hadin spices dina na zuba akai nasake sa maggi guda 2 sai na debo ruwa rabin karamin kofi na zuba.

  6. 6

    Na juya na rufe zuwa minti 10 nasauke karki manta lokacin dahuwan ganda anasa gishiri da citta shikenan

  7. 7

    Sai shinkafa na wanketa nazuba a ruwan zafi dana dora a tukunya tare da gishiri da pis Nabarta ta dahu ba sosaiba amma dai saura kadan tayi, sai na zuba carrot wanda na kankare nawanke na yankashi slice Na dauko gwalanda natace shinkafa dama ya kasance ruwan kinsashi dayawa, sannan nasake mayar da ita cikin tukunya narufe Narage wuta sosai na turarata zuwa wasu yan mintuna Finish

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Jauhar Mukhtar Yusuf^jcuisine
rannar

sharhai

Similar Recipes