Tuwon dawa da miyar zogale,shuwaka da gyada

Maryam Faruk
Maryam Faruk @cook_19343535
Sokoto

Yanada dadi sosae kuma hadin miyar hadi ne dake qara lapiya dakuma jini musamman danasa wake.

Tuwon dawa da miyar zogale,shuwaka da gyada

Yanada dadi sosae kuma hadin miyar hadi ne dake qara lapiya dakuma jini musamman danasa wake.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Dawa
  2. Rogo
  3. Shuwaka
  4. Zogale
  5. Wake
  6. Gyada
  7. Tattasai,tarugu da albasa
  8. tafarnuwaDaddawa,citta,diyan miya dakuma
  9. Manja
  10. Spices
  11. Kanwa
  12. Nama

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Dafarko zaki surfa dawarki ki markada kitankade kisamu nikaken rogo kihadesu,kidora ruwa kan tukunya idan suntafasa kiraba garinki 2 kikwaba rabi kisa muciya kiyi talgi harsai yayi kizuba jiqaqqar kanwarki kirupe kibashi lokaci.

  2. 2

    Idan yadahu kidauko sauran garinki kidinga xubawa har yayi iya kaurin dakikesonae sekirufe kibashi lokaci

  3. 3

    Idan yadahu kisauke kituke sannan kikwashe.

  4. 4

    Idan zakihada miyarki kitafasa namanki,kixuba manja kizuba namanki kisoya sannan kixuba markadaddun kayan miyarki kibarshi yasoyu,kisurfa wake kiwanke kibarshi yajiqa etakuma gyada kidake kixuba cikin soyayyun kayan miyanki kiyita soyawa har yayi sannan kixuba wake.

  5. 5

    Idan yayi kizuba ruwa dakuma ruwan namanki,kizuba dakakkun kayan yajinki da spices kibarta tadahu,kigyara zogale dakuma shuwaka kiwanke shuwakarki saboda daci,sekixuba zogale dakuma shuwakarki kibasu lokaci,idan tayi kikwashe.....enjoy😋

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Maryam Faruk
Maryam Faruk @cook_19343535
rannar
Sokoto

sharhai

Similar Recipes