Tuwon Masara Da Miyar Shuwaka

Zee World
Zee World @Zeeworld

Miyan shuwaka nada amfani wa iyali. Na dafa manane Saboda muna sha'awa kuma yyi ddi ba laifi😋

Tuwon Masara Da Miyar Shuwaka

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin

Miyan shuwaka nada amfani wa iyali. Na dafa manane Saboda muna sha'awa kuma yyi ddi ba laifi😋

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

1 hr
3 yawan abinchi
  1. Garin Masara
  2. Kanwa
  3. Shuwaka
  4. Sant leaf
  5. Ganda
  6. Ice Fish
  7. Manja
  8. Tumatur
  9. Tattasai
  10. Attarugu
  11. Albasa
  12. Garlic
  13. Thyme
  14. Maggi

Umarnin dafa abinci

1 hr
  1. 1

    Da fari, na daura ruwa saina tankade gari na ajiye shi gefe.

  2. 2

    Bayan ruwa y tafasa saina dauko garinnan nayi talge, saina diga kanwa kadan na juya. Ban rufe murfin tukunya ba saboda karya zube. Natafi na bashshi yyita dahuwa. Bayan wani lokaci sai naje na tuka na rage wuta. Bayan yyi nasake tukawa saina sauke na kukkulla.

  3. 3

    Na gyara shuwaka na jikata a ruwa, nasa hannu nayita durzata kaman ina wanki. Nayitayi ina zubda ruwa Ina sake wani ina durzata har saida naji ta daina 'daci tukum. Saina duddunkule ta na yanka sant leaf kanana saina hadasu na ajiye su gefe.

  4. 4

    Dama na tafasa ganda. Na wanke ice fish na tsane na ajiye shi gefe. Saina yayyanka kayan miya kanana. Na jajjaga garlic. Nasa manja a tukunya nasa albasa na jujjuya saina zuba kayan miya Ganda, thyme, garlic na soya. Bayan y soyu saina zuba ruwa amma kadan saboda Ganda nada karfi. Bayan ruwan y sake tsotsewa saina zuba shuwaka nasa maggi da dan gishiri na juya nasa ice fish saboda baida karfi shi. After some mints saina sauke shikenan miyan shuwaka ta kammala🤗😋.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Zee World
Zee World @Zeeworld
rannar

sharhai

Similar Recipes