Fish roll

#FPPC yarana suna son fish roll sosai kuma nakanyimusu lkci zuwa lkci sai nasamu sabon recipe wurin maryams kitchen sai nace bari nagwada. Nayi kuma naji dadinsa nida iyalaina harda wasu daban
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki tankade flour kixuba a roba sai kisa baking powder gishiri da sugar kijujjuya sannan kisa butter ki mursika sosai sannan kisa kwai da ruwa sai kwabawa. Zakiyi kwabin kamar na meatpie ko doughnut. Bayan kinkwaba sai kirufe ki ajiye a gefe
- 2
Sai kiwanke kifinki sannan kitafasa sai ki bari yahuce sannan kigyara kicire kayan duka sannan ki mursika tazama kanana sai ki ajiye agefe
- 3
Sai kidaura pan a wuta sannan kisa mai chikali uku zuwa hudu sannan kizuba albasan da kika yanka kidan jujjuya sai ki jajjaga tafarnuwa da citta kizuba akai kijujjuya kibarta nadan lkci sannan kizuba jajjagen attarugu
- 4
Bayan kinzuba attarugu kijujjuya sai kidauko kifin kixuba akai kisake jujjuyawa sai kisa maggi da sauran sinadaran kisake jujjuyawa sai kizuba lawashi kijujjuya sannan kisa koren tattase kijujjuya sai kibari yadahu sai kisauke ki ajiye agefe
- 5
Sai kidauko dough naki kisake kwabawa sannan kiraba gida biyar sai kidau daya kimurza tayi fadi sai kidau wuka kirabashi biyu sannan kidauko hadin kifin kixuba a dayan gefen
- 6
Sannan kinannade sai kidau wuka kiyankata kamar haka sannan kishafa buttar a baking pan dinki sai ki jejjera akai kamar haka
- 7
Sai kidau chokali mai yatsu ki bubbula saman sannan kifasa kwai daya sai ki kada kishashshafa akai sannan kigasa
- 8
Aci dadi lfy
Yanayi
Wanda aka rubuta daga
Similar Recipes

Bow tie buns


4 in 1 meat pie


Sweet potato croquettes


Shawarma


Aloo puri da miyar yelo kori


Spiral chicken pie


Chinese kubza


Maqlooba rice da shredded beef


Fish roll


Miyar wake


Fanke


Yam kebabs


Fish roll


Fried indomi 2


Milky crackers


Special pancake


Alopuri ll


Gurasa


Chicken bread


Crunchy potato crackers


Dolman


Masan semo


Patera da miyan kwai


Brodi na musamman(special bread


Pita bread


Spicy cracker


Akara pan cake


Brodi mai kirfa(cinnamon bread)


Doughnut


Abincin mutanan cuba

sharhai