Tsiren tukunya

Masu dafa abinci 4 suna shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Naman sa
  2. Kulikuli ( dakakke mai Maggi, gishiri, barkono, citta,
  3. Onga, curry a cikin sa dadai sauran kayan kamshi da kuke so)
  4. Mangyada
  5. Albasa
  6. Ruwa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko dai ga kuli kuli mai kayan hadi a ciki, sai ruwa da albasa na yanka. Sai na tafasa nama namai hadin su Maggi da kayan kamshi ya dahu luguf har ya tsotse ruwan, sai nai ta juya naman har ya Fara kamawa kadan. Sai na juye shi.

  2. 2

    Sai na dora mai a wuta da yayi zafi sai na juye naman naita juyawa.

  3. 3

    Bayan minti biyu na zuba hadin kuli kulin naita juyawa.

  4. 4

    Sai na zuba albasa na yayyafa ruwa kadan na rufe tukunyar.

  5. 5

    Bayan rabin minti na bude na Kara xuba kuli kulin na juya sosai

  6. 6

    Na tabbatar ko ina yaji hadin sai na Kara barbada albasa na juye a faranti.

  7. 7

    Aci dadi Lafiya😋

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Tata sisters
Tata sisters @cook_16272292
rannar
Bauchi State
cooking is one of my best hobby
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes