Tsiren tukunya

Masu dafa abinci 2 suna shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Kaza guda daya
  2. Maggi
  3. Gishiri kadan
  4. Curry Leda daya(Gino)
  5. Albasa
  6. Cabbage
  7. Citta
  8. Ruwa kadan
  9. Dakyakken Kuli Kuli mai hadin su Maggi da komai

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko na wanke kaza ta tsaf. sai na xuba Mata ruwa na yayyanka albasa,na zuba Maggi, gishiri, curry, citta, na dora tafashen a wuta.

  2. 2

    Na barshi ya tafasa sosai har kazar ta shanye ruwan duka, nai ta juya ta sosai taji wuta tukun na sai na sauke ta.

  3. 3

    Gata anan na zuba ta a mazubi.

  4. 4

    Sai na Dora mai kadan a kaskon suya.

  5. 5

    Sai na juye kazar duka nai ta juya wa.

  6. 6

    Bayan man ya shiga ko Ina sai na Fara zuba Kuli kulin Ina juya wa.

  7. 7

    Sai na yayyafa ruwa kadan na yanka albasa na zuba sai na rufe na minti biyu.

  8. 8

    Sai na bude na sake zuba Kuli kulin na gauraya.

  9. 9

    Saina sauke na yayyan ka cabbage da albasa.

  10. 10

    Aci dadi lpia

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Tata sisters
Tata sisters @cook_16272292
rannar
Bauchi State
cooking is one of my best hobby
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes