Cup Cake

@Sarah's Cuisine n Pastries
@Sarah's Cuisine n Pastries @cook_26161801
No 253 Tarauni Qtrs.

Wannan kayan maqulashe ne, ga saukin yi, sannan yana daukar lokaci bai lalace ba.......

Cup Cake

Wannan kayan maqulashe ne, ga saukin yi, sannan yana daukar lokaci bai lalace ba.......

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. 3 cupsFlour
  2. 1 cupSugar
  3. 250 gButter
  4. 6Egg
  5. 1 tspBaking powder
  6. 1/4 tspBaking soda
  7. Butter milk ½cup (zabi/ optional)
  8. Flavour 1tsp (vanilla ko Wanda kike so)
  9. Gishiri ½tsp (in kina so)

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ki tankade flour, gishiri, baking powder da baking soda a mazubi me kyau ki hade su.

  2. 2

    Ki saka butter da sugar a mazubi me kyau ki buga, in kina da na'ura mixer kiyi mixing har sai sunyi hade sunyi laushi.

  3. 3

    Sai ki dauko kwanki ki riqa fasawa daya bayan daya kina juyawa a cikin hadin butter din har ya hade. Idan zakisa butter milk din sai ki zuba.

  4. 4

    Sai ki kawo tankadaddiyar flour ki zuba kadan kadan kina juyawa har ki gama.

  5. 5

    Sai ki kawo flavour ki zuba. Ki juya. Zaki iya sa busasshen inibi.

  6. 6

    Sai ki jera takardar ki a mazubin gashi me kamar tanda sannan ki riqa diban hadin kina zubawa kamar cokali daya ko daya da rabi. In kin kammala sai ki gasa.

  7. 7

    Za a iya ci da shayi ko lemu.

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
@Sarah's Cuisine n Pastries
rannar
No 253 Tarauni Qtrs.

sharhai

Similar Recipes