Alelen wake

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki surfa wake ki wanke ki yanka albasa kisa tattasai da tafarnuwa ki Kai markade

  2. 2

    In anka markado maki shi,sai kisa gishiri kadan, ki bukata sosai dan kar tayi kumfa idan kika dafata. Sai kisa manja da man gyada kisa maggi, onga, crayfish sai ki juyata ta hade sosai. Ki dandana kiji komai yajine ko yana bukatar ki kara.

  3. 3

    Sai kisa ruwa daidai kaurinda kikeso. Daman ki dafa kwai sai ki bare kiraba 2. Sai ki debo kullun waken kizuba a leda kidauki rabin kwai kisa ki kuma saka kifi sai ki daure bakin ledan, haka nan zakiyi tayi har sai ya kare

  4. 4

    Ki daura tukunyar kisa ruwa mai dan yawa kadan, sai ki jefa kullin alelenki acikin tukunyar, ki rufe kirif yarufu, kibarshi yayi ta dahuwa sai ta nuna ki sauke.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Aisha Ardo
Aisha Ardo @cook_26614272
rannar
Abuja Nigeria

sharhai

Similar Recipes