Kayan aiki

1 hr da 30 min
4 yawan abinchi
  1. 3Barzajjiyar Shinkafa kifi
  2. Zogale, albasa yankakkiya
  3. Albasa, attaruhu, tafarnuwa da danyar cittar
  4. Kayan kamshi da kayan dandano
  5. Gyada
  6. Mai
  7. Cabeji
  8. Karas
  9. Koren wake da Koren tattasai
  10. Tukunyar pressure pot

Umarnin dafa abinci

1 hr da 30 min
  1. 1

    Dafarko za'a kai inji a barzo Shinkafa, idan aka kawo dai a jikata na tsahon minti goma, sai a Wanketa a tsane ta.

  2. 2

    Sai a zuba mata Mai a Cakuda sosai sai zuba a leda a kulle, a dora tukunyar pressure pot a wuta sai a Tsoma wannan salon da aka kulle a Leda sai a bashi kamar awa daya.

  3. 3

    Mataki na gaba kuma shine, za'a dauko Tsogale a garashi a wanke tas a ajiye a gefe. Sai a dauko sauran vegetables din a yayyank, a jajjaga attaruhu, albasa, danyar citta da tafarnuwa.

  4. 4

    Idan dambu yayi za'a ji yana Kamshi. Idan an sauke sai a zuba a babban mazubi, sai a kuma zuba mai, kayan dandano da kayan kamshi. Asuba wannan jajjagagen su attaruhu. Asuba Gyada da sauran vegetables din.

  5. 5

    A jujjuya da kyau a tabbatar ko ina yaji kayan hadin. Sai a kuma juyewa a Leda a mayar dashi cikin pressure pot. A bashi Minto 15 ya dada turaruwa sai a sauke asuba aci.

  6. 6

    Karin bayani : za'a iya hadawa da soyayyen kifi ko Pepperd chicken ko Duk wani nau'in abinda kakeso kahada kaci dashi.

Yanayi

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan

sharhai (2)

Meenat Abubakar
Meenat Abubakar @A389295
Za'asa ruwa a tukunya lokacinda kazuba a leda

Wanda aka rubuta daga

Askab Kitchen
Askab Kitchen @askab24617
rannar

Similar Recipes