Jellop din taliya a saukake

Askab Kitchen
Askab Kitchen @askab24617

#oneafrica Wannan girki yana da dadi da saukin sarrafawa. Iyalina suna jin dadinsa.

Jellop din taliya a saukake

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan

#oneafrica Wannan girki yana da dadi da saukin sarrafawa. Iyalina suna jin dadinsa.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

minti talatin
mutane 4 yawan abinchi
  1. 1taliyar pasta guda
  2. Tattasai guda biyar
  3. Tumatir manya guda uku
  4. Attaruhu guda biyar
  5. Albasa manya guda biyu, tafarnuwa da danyar citta
  6. Mai ludayi daya
  7. Kayan dandano da kayan kamshi
  8. Garin kori
  9. Ruwa
  10. Dafaffen kwai
  11. Kokomba

Umarnin dafa abinci

minti talatin
  1. 1

    A hada kayan Miya a markada. A samu tukunya a dora akan wuta a zuba mai yayi zafi sai a zuba yankakkiyar albasa adan soya na minti biyu sai a zuba kayan Miya a asoyasu. Idan suka soyu sai a zuba ruwa daidai yadda zai Dafa taliyar.

  2. 2

    Idan ruwan ya tafasa sai a zuba taliyar wadda aka gutsurata, a zuba kayan dandano da kayan kamshi, a zuba garin kori.

  3. 3

    A rufe tukunyar a barta da dahu amma kar a barta tayi luguf.

  4. 4

    Asamu mazubi mai kyau mai tsafta azuba, a yanka dafaffen kwai asaka akai. A yanka kokomba ayi ado da ita.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Askab Kitchen
Askab Kitchen @askab24617
rannar

sharhai

Similar Recipes