Soyayyar taliya

Rushaf_tasty_bites
Rushaf_tasty_bites @snacks_plugkn
Kano State

Soyayyar taliya takasance daya daga cikin abincikan danakeso musamman ma da daddare,saboda batada nauyi kamar yanda yazo a lafitance ma anfison cin abinci mara nauyi da daddare,nakanyita sosai ta hanyoyi daban daban,Amman wannan itace hanya mafi yawanci danakeyi saboda tafi dadi dakuma sauki👌saboda haka naji dadin wannan gasa,domin da itane zanji saukin raba wannan soyayyar taliyar tawa da dukkanin yan uwana🤗sai kun gwada kukansan na kware#team6dinner

Soyayyar taliya

Soyayyar taliya takasance daya daga cikin abincikan danakeso musamman ma da daddare,saboda batada nauyi kamar yanda yazo a lafitance ma anfison cin abinci mara nauyi da daddare,nakanyita sosai ta hanyoyi daban daban,Amman wannan itace hanya mafi yawanci danakeyi saboda tafi dadi dakuma sauki👌saboda haka naji dadin wannan gasa,domin da itane zanji saukin raba wannan soyayyar taliyar tawa da dukkanin yan uwana🤗sai kun gwada kukansan na kware#team6dinner

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Talatin (mintun
Hudu(mutane)
  1. Taliya leda daya
  2. Sausage(dogon nama)guda uku
  3. Karas manya guda hudu
  4. Kokumba guda daya
  5. Albasa Manya hudu
  6. Attaruhu
  7. Kori 1tblsp
  8. 1 tbspKayan kamshi
  9. Maggi (onga) guda daya
  10. 7Maggi(star) guda
  11. Mai na gyada
  12. Tafarnuwa(ta gari)

Umarnin dafa abinci

Talatin (mintun
  1. 1

    Wayannan ne kayan da muke bukata duka

  2. 2

    Zamu zuba mai kadan a tukunya idan yadanyi zafi kadan saimu zuba taliyarmu mu juyata kamar haka

  3. 3

    Muyita juyata har saita chanza kala kamar haka,ta koma kalar ruwan kasa,saimu samu mataci mu tace ta mu aje a gefe

  4. 4

    Agefe dama mun jajjaga attaruhunmu mun yanka albasanmu,karas,kokumba,da dogon namanmu kamar haka

  5. 5

    Saimu dakko tukunya mu dora a wuta mizuba mai kadan kamar haka,saimu zuba jajjagaggen attaruhunmu muzuba albasanmu amman ba duka zamusa albasarba zamu rage kadan

  6. 6

    Muzuba karas,muzuba dogon namanmu saimu juya kamar haka

  7. 7

    Saimu zuba maggi star guda daya mujuya mu rufe yayi kamar minti biyu

  8. 8

    Saimu zuba ruwa kadan mu rufe yayi minti biyu shima,saimu dakko soyayyar taliyarmu mu zubata

  9. 9

    Saimu juya,mu dakko currynmu da magunanmu(star&onga) muzuba

  10. 10

    Saimu juya mirufe kamar minti goma saimu bude muzuba ragowar albasanmu dama da muka ajiyeta,(zesa girkin qamshi sosai)

  11. 11

    Saimu juya mu rufeta tayi kamar minti sha biyar

  12. 12

    Shikenan mungama taliyanmu mu yayyanka mata kokumba akanta saimucita cikin jin dadi da annushuwa ga qamshi👌😋

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Rushaf_tasty_bites
Rushaf_tasty_bites @snacks_plugkn
rannar
Kano State
Its not a big deal for me to write a whole note for my luv with cooking......I love cooking food more than expectation.
Kara karantawa

Similar Recipes