Chocolate da red velvet cake

Afaafy's Kitchen
Afaafy's Kitchen @mohana10
Kano

#nazabiinyigirki
Cake nau'i ne na kayan zaqi da ake cewa dessert da turanci. Ana cinshi bayan an gama cin abinci mai gishiri da a samu daidaiton dandano a harshe kuma suna da dadi sosai,sannan ana yinsu dandano daban daban.
Na yi wannan cake din ne wa kaina da sauran 'yan gdanmu, amma mu ma ba qa'ida muke bi ba😂mun ji dadinshi sosai.
Bayan an gama gasa cake din kamar yadda na yi bayani a qasa kar a yi garajen cireshi daga gwangwani a take, a barshi ya gama hucewa gaba daya dan gujewa fashewa.

Kara karantawa
Gyara girkin
See report
Tura

Kayan aiki

hr 2 da min 30m
6 yawan abinchi
  1. Kofi uku na fulawa
  2. Kofi daya da rabi na sugar
  3. 1daya na baking powder da baking soda Tsp
  4. Kofi daya na mai ko narkakken butter
  5. Kofi daya da rabi na buttermilk
  6. Qwai biyu
  7. 1da rabi na food color ja Tsp
  8. 3na cocoa powder Tbsp
  9. Babban cokali daya da rabi na flavor
  10. Kayan hadin chocolate cake
  11. Kofi daya na flour
  12. Rabin kofi na cocoa powder
  13. Rabin qaramin cokali na baking soda
  14. Qaramin cokali na baking powder
  15. Kofi daya na sugar da dan gishiri kadan
  16. Qwai daya
  17. 1/4kofi na mai ko narkakken butter rabin kofi
  18. Rabin kofi na buttermilk
  19. Rabin kofi na coffee mai dumi sosai
  20. Rabin cokali flavor

Umarnin dafa abinci

hr 2 da min 30m
  1. 1

    Za mu fara da red velvet, da farko za a tankade flour a roba/kwano, a zuba sugar, cocoa powder da food coloring na gari, a taqaice dai duk busassun ingredients a hadu waje daya a jujjuya.

  2. 2

    Sai a zuba jiqaqqun ingredients daya bayan daya, su buttermilk, qwai, mai da flavor, sai a yi amfani da whisker ko mixer a cakudeshi da kyau a ajiye gefe

  3. 3

    Chocolate cake ma za a tankade flour, cocoa powder baking powder da soda, sai a zuba sugar da dan barbaden gishiri kadan a cakude,

  4. 4

    Sai a zuba butter milk,mai,qwai,flavor da coffee, a yi whisking a hankali ya hade jikinshi duka

  5. 5

    Sai a shafe gwangwanin cake din da butter a dan barbada flour ayi coating da kyau,saboda ya sauqaqa cirewa bayan an gasa. Sai a juye kwa6in a gasa a oven din da aka yi pre-heating.
    Na qawata nawa da whipping cream,dagargajen cake da sprinkles.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan

Wanda aka rubuta daga

Afaafy's Kitchen
rannar
Kano

Similar Recipes

More Recommended Recipes