SHINKAFA DA WAKE DA YAJIN KULI-KULI

Rukayya Jarma
Rukayya Jarma @ruky14744

A shekarun baya Ana cin SHINKAFA da wake da yajin kuli kuli Maimakon yajin barkono#GARGAJIYA

SHINKAFA DA WAKE DA YAJIN KULI-KULI

A shekarun baya Ana cin SHINKAFA da wake da yajin kuli kuli Maimakon yajin barkono#GARGAJIYA

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

mutum hudu
  1. Shinkafa Kofi uku
  2. Wake kofi biyu
  3. Kuli kuli
  4. Mai
  5. Barkono
  6. Maggi
  7. Gyadar miya
  8. Gishiri
  9. Salak
  10. Tumatur albasa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ki gyara wakenki ki zuba ruwa a tukunya ki Dora in ya tafasa ki zuba waken a ciki ki rufe har Sai ya kusa dahuwa

  2. 2

    Ki wanke shinkafa ki zuba su dahu tare,in sun dahu ki Samu abin tace taliya ki tace ruwan daya rage ki maida ta karasa tsanewa ki juye a flast

  3. 3

    Ki zuba kuli kulinki a turmi da barkono, Maggi, gishiri da Kuma gyadar miya ki dakasu har suyi laushi ki kwashe a roba ki rufe

  4. 4

    Ki soya Mai da albasa,ki yanka salak da tumatur hade da albasa,in Kika zuba wake da shinkafarki a plate saiki kawo Mai da yajinki ki zuba ki kawo hadin salak ki zuba akai.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Rukayya Jarma
Rukayya Jarma @ruky14744
rannar
Ina kaunar girki musamman snacks da Kuma Miya kala kala
Kara karantawa

sharhai (3)

Similar Recipes