Shinkafa da wake

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

2hrs
4 yawan abinchi
  1. Shinkafa,Kofi uku
  2. Wake Kofi daya
  3. Kanwa ungurnu rabin cokalin shayi
  4. Gishiri rabin cokalin shayi

Umarnin dafa abinci

2hrs
  1. 1

    Da farko Zaki gyara wakenki ki wanke shi

  2. 2

    Saiki samu tukunyar ki ki zuba ruwa daidai yanda Zaki dafa wake da shinkafarki ki dora akan wuta

  3. 3

    Ki zuba waken a ciki saiki zuba kanwa da gishiri ki juya

  4. 4

    Sannan ki rufe ki barshi sai yayi rabin dahuwa sannan Zaki wanke shinkafa ki zuba ki juya ki barta ta kusa dahuwa

  5. 5

    Sannan ki tace,saiki maida ta cikin tukunyar ta turara

  6. 6

  7. 7

    Saiki sauke shikenan an gama wake da shinkafa

  8. 8

    Sannan na tsane a kwando sannan na dakko Mai da yaji na da soyayyen kifi na na zuba akai kamar yanda kuka gani a hoto,

  9. 9

    Da fatan zaku gwada yanda nakeyin wake da shinkafa na da Mai da yaji wato garau-garau

  10. 10

    A gefe Kuma na gyara salad dina na wanke shi da gishiri na kara wanke shi da ruwa

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Hygienic Snacks and Spices kn
rannar
I love cooking and making snacks
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes