Shinkafa da wake garau garau

Garau garau inji malam bahaushe ga dadi ga Gina jiki wollah ga saukin girkawa#garaugaraucontest
Shinkafa da wake garau garau
Garau garau inji malam bahaushe ga dadi ga Gina jiki wollah ga saukin girkawa#garaugaraucontest
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko uwar gida ko amarya zaki tsince shinkafar ki idan ta hausace idan kuma ta bature ce shikenan,in kin tsince ki ajeye agefe
- 2
Sai ki dauko wakenki shima ki tsince duk wani datti da kwarin wake shim ki ajeye agefe
- 3
Sai ki kunna murhu ko gas duk Wanda Allah ya hore miki uwar gida,sai ki daura tukunyar ki mai dauke da ruwa aciki sai ki rufe idan ya tafasa sai ki zuba wakenki ki saka kanwarki da kishiri kadan sai ki saka siga sai Ki rufe Kamar minti 30
- 4
Idan wakenki ya dahu sai ki dauko Ki daura tukunyar shinkafa, ki daura tukunyar ki mai dauke da ki daura kan gas ko murhu idan ruwan ya tafasa ki zuba shinkafarki sai ki zuba gishiri kadan da man gyada kadan Dan zai taimakawa shinkafarki tayi lafa lafa tayi kyau karki zuba ruwa dayawa awajen dahuwar shinkafar, shinkafarki tana dahuwa sai ki sauke.
- 5
Ki daura kaskon suyan man gyada ko man ja, ki zuba manki a kasko tare da albasa ki soya karki bari yayi baki ita albasar
- 6
Zai ki dauko salad da tumatir dinki ki wanke shi ki yanka irin yankan da kike so.
Cooksnaps
Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!
Similar Recipes
-
Shinkafa da wake(garau garau)
Yauma na sake dawowa da garau garau amma da farin wake wannan karan #garaugaraucontest Fateen -
Shinkafa da wake
Wato duk wani asalin bahaushe yasa Shinkafa da wake ( garau garau) ana girmama Shinkafa da wake ne bisa alfanun da take a jikin mutum mussàm ma wake yana Gina jiki #garaugaraucontest Fateen -
Garau garau (shinkafar da wake)
Zan Iya kin cin komai amma banda garau garau, zan Iya cinta awa ishirin da hudu. Ga dadi ga amfani a jikin mutum#garaugaraucontest Fateen -
Garau garau
Shinkafa da wake abinci ne me Gina jiki musamman wake yana kara lfy da kuzari ajikin mutum,sannan kuma abinci ne ga ko wane bahaushe yake shawaarsa #garaugaraucontest Zhalphart kitchen -
Garau garau
Garau garau abincin rana a kasar Hausa, musamman ma idan taji kayan hadi irin haka, baa bawa yaro mai kyuya. Garau garau tana da farin jini wajen al’umma, Ga saukin dafawa, ga dadi a baki, ga kara lafiya, ga kuma sa koshi. #garaugaraucontest Cakeshub -
Garau Garau
Garau Garau girkine na gargajiya Wanda muka gada tun iyaye da kakanni......garau garau abincine mai daukeda sinadarai masu gina jiki gakuma fadi dayake dashi....shiyasa naso na raba wannan kayataccen girki nawa na gargajiya (garau garau) daku.....bayan haka mahaifina ya kasance mason garau garau shisa nima nakesonta kunga kuwa abinda kakeso ka sowa Dan uwanka😘#garaugarauconteste Rushaf_tasty_bites -
Shinkafa da wake (garau garau)
Garau garau abincin hausawa ne musamman wadanda suke a kano. Ina mutukar son garau garau domin shine abincin dana fi so naci yana d dadi sosai.xaki iya cinta da mai d yaji ko miya #garaugaraucontest# Salma's_delicacies. -
-
Shinkafa da wake(garau-garau)
Shinkafa da wake abincin hausawane mae farin jini sosae,gashi baa kashe wasu kudi masu yawa gurin yinsa amma sae dadi,duk jumaa sae naci garau-garau 😂😍😋#garaugaraucontest Firdausy Salees -
Shinkafa da wake (garau garau)
Shinkafa da wake yana daya daga cikin abincin da nafiso a duk sanda zan dafa ina acikin farinciki musamman irin dahuwar da kakata takeyi#garaugaraucontest Fateen -
Shinkafa da wake(garau-garau)
#garaugaraucontest. shinkafa da wake abincin hausawane mae dadi da farin jini,gashi kowa nasonsa,abincine da baa kashe kudi da yawa gurin yinsa amma sae dadi,ni bana wuce tayin garau-garau koda na koshi😂😂 Firdausy Salees -
-
Garau garau (shinkafa da wake)
Shinkafa da wake ko garau garau abinci ne da aka fi sani ya shahara a arewacin nigeria ana ci da mai da yaji da maggi sannnan akan iya qara wasu abubuwa domin dadin ci kamar su kifi da salak da sauran su shi ake kira (garau garau) #garaugaraucontest Ayyush_hadejia -
-
Shinkafa da wake(garau garau)
Khady Dharuna #garaugaraucontest Garau garau tana daya daga cikin abincin hausawa da akafi so, wasu don kwadayi sukeyi Wanda mafi yawa anfiyi don abincin yau da kullum. Haka zalika yarana Suna sonta sosai... Khady Dharuna -
-
-
Garau garau da coselow
Garau garau da coselow akwai dadi cikayi Santo kenan #garaugaraucontest Meenat Kitchen -
-
Garau garau da nama da kwai
Wannan hadin akwai dadi kigwada kawai kiji dadinki #garaugaraucontest Meenat Kitchen -
Garau Garau
Garau Garau abincine me dadin gaske.. Kuma qayatashi na qara jin shawa'ar cinsa.Garaugarau inyasami salad tamatir da yaji me dadi hryafi shawarma dadi😋😋 #garaugaraucontest Ummu Fa'az -
Shinkafa da wake (garau-garau)
Ina son wake da shinkafa, abincine mai kara lafiya ga jiki. Ashley's Cakes And More -
Garau garau girki daga mumeena’s kitchen
#garaugaraucontest Itadai garau garau wato shinkafa d wake abinchi Mai matukar farin juni ga mutanen Hausa musamman taji ganye ka hada d yajinka Mai dadi abinchi ne mai Sanya kuxari d Gina jiki habawa ba'a bawa yaro Mai kiya Yan uwa ga hanya mafi sauki wajen dafa garau garau kuma ki ganta fara Shar muje xuwa mumeena’s kitchen -
-
Garau Garau
Garau Garau abincine da yayi suna musamman ga nahiyar hausawa ,garau garau yana samuwa ne ta hanyar hada shinkafa da wake ,abinci ne mai gina jiki da kara lafiya musamman in an kawata shi da kayan lambu ire iren tumatir da dogon gurji da sauransu,ga saukin dafawa ga kuma gamsawar wa ga wanda yaci! Akwai hanyoyi da dabaru kala kala da ake amfani dasu wajen girka wake da shinkafa wato garau garau ,ni ga yadda nake dafa nawa ! Chef abdul -
-
Shinkafar hausa da wake (Garau Garau)
Ko kin san cewa wake da shinkafa garau garau yafi dadi da shinkafar hausa da soyayen kifi😍😋Matso kusa kisha mamaki Jamila Ibrahim Tunau -
Shinkafa da wake
#GargajiyaGarau garau/ qato da lage abinci ne mai matuqar Dadi ga Gina jiki. Ana ci da miya ko da mai da yàji ko sauce a hada da salad. Walies Cuisine -
-
More Recipes
sharhai (2)