Meat pie

Ayshat Adamawa(U. Maduwa)
Ayshat Adamawa(U. Maduwa) @Ayshat_Maduwa65
Abuja

#pie and yes it’s a pie week. So let’s bake some pies. Ga yadda nake nawa meat pie din wlh dadi ba a magana. Ku gwada ku turamin feedback @jaafar . Also meat pie nason komai da zakayi anfani dashi ya zama mai sanyi

Meat pie

#pie and yes it’s a pie week. So let’s bake some pies. Ga yadda nake nawa meat pie din wlh dadi ba a magana. Ku gwada ku turamin feedback @jaafar . Also meat pie nason komai da zakayi anfani dashi ya zama mai sanyi

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Awa daya da rabi
Mutane biyar
  1. Flour cup hudu
  2. Butter cup daya 250grm
  3. Kwai guda daya
  4. Baking powder chokali daya
  5. Sugar chokali daya
  6. Madara chokali biyu
  7. 3/4 cupRuwa mai sanyi
  8. Sai filling din
  9. Nikakken nama rabin kilo
  10. Dankali guda biyar
  11. Attarugu guda hudu
  12. Shombo guda uku
  13. Maggi yadda ake bukata
  14. Albasa manya guda biyu
  15. Man gyada
  16. Carrot,
  17. Koren tattase, scent leave
  18. Garlic da ginger chokali daya
  19. Spices duk wadda kike son
  20. Curry da thyme madaidaici
  21. Cornflour chokali daya

Umarnin dafa abinci

Awa daya da rabi
  1. 1

    Da farka zaki fara da tankade flour a bowl sai ki zuba butter, baking powder, madara,sugar,sai kiyi mixing dinsu da kyau

  2. 2

    Daga nan sai ki fara kwanki guda daya ki zuba ruwa mai sanyi ki kwaba dashi.

  3. 3

    Daga nan saikisa a fridge

  4. 4

    For the filling kuma. Daman kin Riga da kin nika namarki sai ki samo tukunyarki kisa a wuta tareda mai, albasa, garlick da ginger sai ki dan soyasu sama sama

  5. 5

    Daga nan sai ki zuba nikakken naman ki soyashi.

  6. 6

    Sai ki zuba ruwa ki zuba Kayan dandanen ki da kikeson.

  7. 7

    Idan kinason zaki iya dafa dankalinki da carrot daban idan naman tayi sai ki zuba akai ki gauraya. Idan kinaso kuma zaki iya zuba su veggies din tare da naman su nuna tare

  8. 8

    Daga nan sai ki zuba su attarugunki ki chakuda da kyau. Anan sai ki kwaba cornflour dinki da dan ruwa ki zuba akai

  9. 9

    Daman kin Riga da kin yayyanka koren tattarenki da ganyen albasa da dan scent leave to sai ki zuba akai. Hmmmmmmm wannan hadin ko ba a cewa komai sai ka gwada

  10. 10

    Kinga yadda filling dinmu ya kasance

  11. 11

    Daga nan sai ki fitar da dough dinki daga fridge Daman filling din na yayi sanyi sai kiyi rolling dinshi

  12. 12

    Saiki zuba hadin akan cutter din

  13. 13

    Sai ki shafa flour ko egg a bakin kamar haka

  14. 14

    Sai ki rufe bakin ki yanka sauran dough na bakin

  15. 15

    Gashinan mun gama. Ji yadda yayi kyau a ido

  16. 16

    Sai ki jera a baking tray.

  17. 17

    Sai kiyi egg wash dinshi

  18. 18

    Sai ayi baking

  19. 19

    Har sai yayi color da kikeson. Idan Ina meat pie ina egg wash sai biyu ko uku. Kafin nasa a oven zanyi idan ya fara gasuwa zanyi kam na kunna wutan sama shima zanyi wannan shine stirring baking dina🤩

  20. 20

    Dan Allah kiga meat pie din nan

  21. 21

    Gashinan bayan na gama baking kam

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Ayshat Adamawa(U. Maduwa)
Ayshat Adamawa(U. Maduwa) @Ayshat_Maduwa65
rannar
Abuja
cooking is my dream and also cooking is all about being creative
Kara karantawa

Similar Recipes