Plantain da wake

Khadija Habibie
Khadija Habibie @cook_37541917

wannan hadin zai Dade achikin ka kafin kaji yunwa ga dadi ga riqon chiki#wake

Plantain da wake

wannan hadin zai Dade achikin ka kafin kaji yunwa ga dadi ga riqon chiki#wake

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

3 yawan abinchi
  1. 2 cupWake
  2. 2Plantain
  3. 1Kwai
  4. Tattasai,attarugu,albasa
  5. Kayan Dan dano
  6. Kayan qanshi
  7. Ruwa
  8. Mai

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki wanke plantain sannan ki yanka ta ki saka gishiri kadan ki saka Mai awuta idan yayi zafi saiki fara soyata har tayi yanda Kike so saiki sauke

  2. 2

    Zaki gyara wake sannan ki wanke shi ki saka awuta ki saka ruwa ki saka baking powder da albasa ki rufe har yayi idan ya kusa yayi saiki saka tattasai attarugu da kayan Dan dano dana qanshi ki saka kafi likita akai idan yayi saiki sauke

  3. 3

    Zaki daukho dafaffen kwai ki yanka akai shike nan achi dadi lafia

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Khadija Habibie
Khadija Habibie @cook_37541917
rannar

sharhai

Similar Recipes