Masa (waina)

Masu dafa abinci 4 suna shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. kanwa dan kadan
  2. ahinkafan tuwo kofi biyar
  3. shinkafan tuwa rabin kofi (wanda zaki dafa)
  4. yis chokali daya babba
  5. siga yanda zai ishekk
  6. man gyada

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki wanke shinkafa da daddare kisa ruwa aciki,idan kin tashi da safe sai ki dafa rabin kofin shinkafan ya nuna ki barshi yasha iska

  2. 2

    Sai ki tsiyaye ruwan shinkafan da ya kwana kisa wanda kika dafa ki kai nika idan an dawo sai ki sa yis ki juya sosai sai kisa aguri me dumi dan ya tashi

  3. 3

    Zaki jika kanwa da ruwa,idan ya tashi sai kisa ruwan kanwa da siga ki juya,kisa tandan waina akan wuta idan yayi zafi kisa man gyada sai kisa kullin aciki ki soya idan yayi sai ki juya daya gefan haka zakiyi har ki gama, za aci da miyan taushe

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Amina Aminu
Amina Aminu @cook_13830126
rannar
zaria,kaduna state

sharhai

Similar Recipes