Dan waken gargajiya

Salwise's Kitchen
Salwise's Kitchen @cook_16516066
Zaria

#dan-wakecontest,ina son dan wake,musamman Wanda akayi shi a gàrgajiyance,domin ingañcinsa a jikin mu da lafiyàr mu. Shiyasa nima na hada nawa na gargajiya. Gà dadi ga dàndano.

Dan waken gargajiya

Masu dafa abinci 3 suna shirin yin wannan

#dan-wakecontest,ina son dan wake,musamman Wanda akayi shi a gàrgajiyance,domin ingañcinsa a jikin mu da lafiyàr mu. Shiyasa nima na hada nawa na gargajiya. Gà dadi ga dàndano.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Minti ashirin
Hudu
  1. Garin alabo gwangwani hudu
  2. Garin dawa gwangwani biyu
  3. Garin wake cokali biyu
  4. Kuka karamin cokali daya
  5. Ruwan kanwa kadan
  6. Ruwan kwabawa
  7. Mangyada
  8. Yaji
  9. Tumatur
  10. Cucumber
  11. Kabeji
  12. Magi

Umarnin dafa abinci

Minti ashirin
  1. 1

    Ga kayan hadin mu kamar haka,alabo, kuka, garin wake

  2. 2

    Ga sauran kayan hadin mu,garin dawa dà ungurnu

  3. 3

    Da farko za'a hàda,garin alabo,garin dawa da kuka, sai azuba ruwan kanwar/ungurnu daidai,sai a zuba ruwa a ajujjuya su hade kamar yadda ake gani a hotunan

  4. 4

    Gashi bayan sun hadu

  5. 5

    Sai a Dora ruwa a wuta, idan ya tàfasà,sai a rika gutsirar kwabin dan waken ana sakawa har agàma

  6. 6

    Sannan a rufe a barshi ya nuna na tsahon miñti ashirin

  7. 7

    Sai a kwashe a zuba cikin ruwan sanyi,a dauraye domin kàwàr da dankon

  8. 8

    Sai a tsame,a zuba a màzubi,a yanka tumatur, cucumber da kabeji

  9. 9

    À toyà mangyada da albasa,a sanya yaji da magi.Ga sàkamakon aci lafiya.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Salwise's Kitchen
Salwise's Kitchen @cook_16516066
rannar
Zaria
I was born and bred up in Zaria
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes