Dafadukar Indomie da Dankali

Sadiya Taheer Girei
Sadiya Taheer Girei @cook_15214700
Bauchi

#SSMK wannan dai girki ne na kowa da kowa dan manya da yara duk suna son indomie, na hada ta da dankali ne dan karin armashi😍

Dafadukar Indomie da Dankali

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin

#SSMK wannan dai girki ne na kowa da kowa dan manya da yara duk suna son indomie, na hada ta da dankali ne dan karin armashi😍

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

minti ashirin
daidai dafawark
  1. Dankali kadan
  2. Indomie guda biyu
  3. Tattasai
  4. Albasa
  5. Ruwa
  6. Maggi
  7. Mangyada
  8. a

Umarnin dafa abinci

minti ashirin
  1. 1

    Da farko dai na debo dankalina ne na fere shi na yanka kanana sannan na wanke shi tas na barshi a cikin ruwa.

  2. 2

    Sannan na debo kayan miyana na wanke a gyara shi sannan na markada shi a greta, daga nan nasa tukunya akan wuta na zuba mai na yanka albasa da mai din yayi zafi saina zuba kayan miyan akai na soya.

  3. 3

    Bayan na soya saina zuba ruwa kamar karamin kofi biyu sannan nasa maggin indomie na kara da maggi star sannan na fara zuba dankalin na rufe bayan ya tafasa kamar minti goma saina zuba indomie na gaurawa na rufe, ya sake yin minti goma saina duba naga ya dafu sannan na sauke...😘

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Sadiya Taheer Girei
Sadiya Taheer Girei @cook_15214700
rannar
Bauchi
I'm Sadiya Taheer based in Adamawa Married in Bauchi,i love cooking food also love to see others food and lean more too😍
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes