Tura

Kayan aiki

  1. Fulawa
  2. Baking powder
  3. Mai
  4. Gishiri
  5. Nama
  6. Attarugu da albasa
  7. Sinadarin dandano
  8. Ruwa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko Zaki tankade fulawarki kicire dattin cikinta saiki zuba a cikin mazubi Mai fad'i saiki zuba gishiri kad'an kizuba baking powder saiki murza idan sun had'e saiki zuba Mai kad'an kicigaba da murzawa idan sun had'e saiki zuba ruwa kicigaba da murzawa saiki dauko Tire Mai fad'i da kwalba sai murza ta kifitarda ita raund idan kingama saiki zuba garin fulawa acikin plate kidauko daya kiaza idan saiki riqa shafa Mai ajikin spoon kishafa idan kinshafa saiki daura d'aya akai ki hk zk tayi,

  2. 2

    Bayan kingama jerasu sai ki aje sai ta tashi kisake murzata da kwalba idan ta tayi Fadi saiki gyara sharp dinta sannan ki yankata gida 4

  3. 3

    Saiki kwaba fulawa Yar kadan da ruwa, saiki riqa lankwasa fulawar can da Kika yanka gida 4 Kika rarrabata da Yan uwanta kiriqa yin kamar sanho kina liqeta da kwababbiyar fulawar kina like saman,

  4. 4

    Bayan kin kammala dama kin tanadi Naman ki da Kika daka da attarugu da albasa da sinadarin dandano bayan kin tafasashi,saiki riqa zubawa acikin waccan sanho kina liqewa da kwababbiyar fulawar,

  5. 5

    Dama kindora Mai awuta yayi zafi saiki riqa daukowa kina tsomawa acikin ruwan man idan yayi kijuya daya baren idan yayi ki kwashe shekenan kin kammala samosa😋😍😘

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Mmn khairullah
Mmn khairullah @cook_18339957
rannar
Sokoto
Ina son girki tun Ina karama,girki kansani nishadi🤩
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes