Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Kifi karfasa
  2. Attaruhu
  3. Albasa
  4. Ginger
  5. Tomeric
  6. Mai
  7. Maggi
  8. Gishiri

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki kankare kifin ki ki yanka cikin ki cire dattin da kayar miki.

  2. 2

    Sai ki gyara albasa ki wanke ki yayyanka a tsaye saiki tsinke attaruhu ki wanke kinjajjaga, saiki daura tukunya ki daura mai in yayi zafi ki juye albasar nan inta fara soyuwa ki gurza tomeric da ginger ki zuba a ciki.

  3. 3

    Saiki jujjuya ki juye attaruhu ki jujjuya saiki zuba ruwa kadan ki saka maggi da gishiri, saiki juye kifin ki jujjuya ki saka murfi ki rufe.

  4. 4

    Tsahon minti 7 zuwa 10 farfesun ki yayi saiki kashe wuta kinjuyea flask.

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Umma Sisinmama
Umma Sisinmama @cook_14224461
rannar
Kano
I was born in kano state
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes