Taliya da miyar ganyen albasa

TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA) @cook_15480513
Port Harcourt

#oct1strush nayi wannan taliyar sbd murnan kasata zatacika shekara sittin da samun yanci

Taliya da miyar ganyen albasa

#oct1strush nayi wannan taliyar sbd murnan kasata zatacika shekara sittin da samun yanci

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Taliya leda daya
  2. Gishiri
  3. Mai
  4. Hadin miya
  5. Albasa babba daya
  6. Danyen tumatur guda biyar
  7. Attarugu yanda kikeso
  8. Soyayyen nama ko kifi
  9. Maggi knorr chicken and beef
  10. Maggi star
  11. Curry thyme and tumeric
  12. Mai
  13. Ganyen albasa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Dafarko zakidaura tukunya a wuta kisa mai idan yayi zafi kizuba albasa kisoyata amma karkibari yasoyu sosai

  2. 2

    Bayan kinsoya albasa sai kijajjaga kayan miyan kizuba kici gaba da soyawa nadan mintuna kadan sannan kixuba maggi dasauran sinadaran dandanon sannan kixuba soyayyen nama dakuma curry thyme da kurkur

  3. 3

    Bayan kinzuba sai kici gaba da soyawa har yagama soyuwa sannan kixuba ruwa kadan akai sai kirufe kibarta yabararraka sannan kiyanka lawashinki kiwanketa dakyau sai kizuba akai kijujjuya kibarta nadan lkci kadan sai kisauke

  4. 4

    Sannan kidaura tukunyar da zaki dafa taliyar da ita a wuta kisa ruwa dadan dama kirufeta yatafasa

  5. 5

    Bayan yatafasa sai kizuba taliyar kibari yatafaso sai kisauke kizuba a madambaci kiwanke sannan kirabata kashi biyu sai kisake maidasu a wuta daban daban sannan kizuba ruwa a kowanne da gishiri sannan kidiga green kala adayan sai kisa mai kadan kirufe kibarsu yadahu shikenan angama

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
rannar
Port Harcourt
Gskiya arayuwata inason girki sosai shiyasa kullum ina kicin wurin tsara abinci kalakala
Kara karantawa

Similar Recipes