Tuwon masara

Walies Cuisine
Walies Cuisine @ummuwalie
Sokoto

Masara nada anfani ga jiki sosai shiyasa can ba'a rasa ba nakan Dan sarrafa ta domin lahiyar iyalina. Masara Tana gyaran fata, cin ta Abu ne Mai anfani ga Mai ciki, Tana qara qarfi, Tana rage sugar jiki wato( blood sugar) da wasu da dama.

Tuwon masara

Masara nada anfani ga jiki sosai shiyasa can ba'a rasa ba nakan Dan sarrafa ta domin lahiyar iyalina. Masara Tana gyaran fata, cin ta Abu ne Mai anfani ga Mai ciki, Tana qara qarfi, Tana rage sugar jiki wato( blood sugar) da wasu da dama.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ki aza ruwa saman wuta a cikin tukunya sai ki jefa kanwa kadan a ciki ki ruhe, idan ya tafasa said kisa butter Kamar babban cokali day, ki samu wuri daban ki dibi garin masara ki kwaba da ruwa kar yayi kauri sosai Kuma kar yayi ruwa sosai. Sai ki dauko hadin garin ki zuba acikin ruwan masu tafasa kina juyawa da muciya kar yayi gudaji Amma Zaki rage wutar idan yayi kauri sai ki rufe ki bashi lokaci ya dahu.

  2. 2

    Idan ya dahu, sai ki raba biyu, ki zuba Rabin a want wuri ki ruhe ki bar Rabin a tukunya ki tuqa kina zuba gari kadan kadan kina tuqawa har kaurinshi yayi Miki sai ki yayyafa ruwa a sama ki ruhe ya qara dahuwa, idan ya dahu sai ki dauko wancan Rabin talgen da Kika aje ki zuba acikin ki tuqa sosai sai ya hade ki qara mintoci kadan ki sauke Amma kar ki Bari yayi qarhi ki Yishi da laushi, sai ki kwashe aci da miyar da akeso Amma yahi Dadi da miyar yauqi.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Walies Cuisine
Walies Cuisine @ummuwalie
rannar
Sokoto
Ummu wali by name, I love creating new recipes and cooking is bae***😍
Kara karantawa

sharhai (2)

Similar Recipes