Danderu

Jamila Ibrahim Tunau
Jamila Ibrahim Tunau @Jamitunau
Sokoto State

Dadewa ina son gwada danderu amma Allah be nufa ba sede yanzu. Na sadaukar da wannan girki ga Zarah Haruna matar Mustapha Ahmad wadda Allah yayi ma rasuwa jiya 7th September 2022 Allah ya gafarta miki zarah

Danderu

Dadewa ina son gwada danderu amma Allah be nufa ba sede yanzu. Na sadaukar da wannan girki ga Zarah Haruna matar Mustapha Ahmad wadda Allah yayi ma rasuwa jiya 7th September 2022 Allah ya gafarta miki zarah

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Awa 24 awa 12 ya kwana fridge 12 bisa wuta
7 yawan abinchi
  1. Wuyan rago (ram neck)
  2. 10Tarugu
  3. 20Tafarnuwa
  4. Citta danya 2 manya
  5. 2Albasa
  6. 15Maggi
  7. 2Ajino moto
  8. 4Lemun tsami
  9. Mixed spice chokali 2
  10. vinegar
  11. Tools
  12. Foil paper
  13. Madambachi/ Steamer
  14. 1Mai luddai

Umarnin dafa abinci

Awa 24 awa 12 ya kwana fridge 12 bisa wuta
  1. 1

    Farko ki jera kayan ki komai ready

  2. 2

    Idan an sawo miki wuyan ki wanke shi tas

  3. 3

    Sannan idan kina da vinegar ki shafe shi da shi tas sannan

  4. 4

    Ki hada duka mixed spice da maggi da ajino moto ki daka a turmi ki yanka lemun tsami ki saka

  5. 5

    Sannan ki shafe naman ki da dukan su kiyi ta murzawa ki tabbata ko ina ya samu shiga se ki saka a leda ya kwana cikin fridge dede komai ya shiga ciki

  6. 6

    Lemun daya zaki matse ruwan ki shafa 2 kuma zaki yanka su neki aza bisa

  7. 7

    Idan ya kwana ki fiddo ki jera foil paper sannan ki saka butter ko mai ki lullube naman ki tas

  8. 8

    Se ki saka ruwa kasan tukunyar ki ki saka naman a tukunyar sama

  9. 9

    Sannan ki rufe zeyi kusan awa 12 bisa wuta kafin kisamu yadda ya kamata

  10. 10

    Akwai yiwar mai ya koma kasan tukunya tareda ruwan se ki tsiyaye ki chanza ruwan

  11. 11

    Kiyi amfani dasu wurin miya

  12. 12

    To masha Allah kinga yadda ya fita masha Allah steamed meat ya kammala

  13. 13

    Zaki iya ci da burodi ko da biryani rice koma da jollof

  14. 14

    Muradi de kiyi enjoying namanki

  15. 15

    Zefi dadin ci da daddare hakan daga ke se megida idan ke amarya ce 😉

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Jamila Ibrahim Tunau
rannar
Sokoto State
The kitchen is my comfort zone.
Kara karantawa

Similar Recipes