Tuwon shinkafa da miya kubewa

khadijah yusuf
khadijah yusuf @cook_25951409

#cks#gargajiya

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

2hrs
4 yawan abinchi
  1. Farar shinkafa
  2. Ruwa
  3. Danyar kubewa
  4. Manja
  5. Tattasai, tumatur da albasa
  6. Maggi
  7. Gishiri
  8. Black pepper

Umarnin dafa abinci

2hrs
  1. 1

    Bayan ruwan ki ya tafasa sai ki wanke farar shinkafar ki zuba.

  2. 2

    Sai ki bari ta dahu tayi laushi Sannan ki tuke da muciya sannan ki mayar kan wuta ta sulala.

  3. 3

    Sai ki Kara tukawa kiyi malmala ki sa a Leda.

  4. 4

    Sai ki soya markaden da manja sannan ki tsaida ruwan miya Sannan ki sa maggi da gishiri sai ki bari su tafasa sannan ki zuba danyar kubewar ki sannan ki bari ta dahu sai ki sauki. Miyar kubewa akwai dadi sosai 😋😋.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
khadijah yusuf
khadijah yusuf @cook_25951409
rannar
Love trying new recipes✨
Kara karantawa

Similar Recipes