Parpesu mai ridi

Salwise's Kitchen
Salwise's Kitchen @cook_16516066
Zaria

#parpesucontest# Wannan hadin parpesu ne na musamman danayi,domin k'aruwar ingancinsa ajikin mu,wannan had'in nada amfani sosai,musamman ga iyaye mata masu jego yana taimaka masu sosai.Sobada anyi shi da kayayyan kamshi masu inganci ga jikin mu,ga kuma ridi, shima yana da inganci.Zanso ace kun gwada wannan kalar parpesun.

Parpesu mai ridi

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin

#parpesucontest# Wannan hadin parpesu ne na musamman danayi,domin k'aruwar ingancinsa ajikin mu,wannan had'in nada amfani sosai,musamman ga iyaye mata masu jego yana taimaka masu sosai.Sobada anyi shi da kayayyan kamshi masu inganci ga jikin mu,ga kuma ridi, shima yana da inganci.Zanso ace kun gwada wannan kalar parpesun.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Away d'aya da rabi
Mutane biyar
  1. Hanta
  2. K'oda
  3. Hunhu
  4. Tumbi
  5. Hanji
  6. Kayan miya
  7. Citta,kanunfari,tafarnuwa,masoro,kimba
  8. Gishiri kadan,ruwa
  9. Garin rid'i
  10. Kori,taim,daddawa,nutmeg(yar miya)
  11. Man gyada,maggi mai d'and'ano

Umarnin dafa abinci

Away d'aya da rabi
  1. 1

    Ga kayayyakin,had'in mu kamar haka

  2. 2

    Da farko,za'a zuba ruwa a tafasa kayan cikin,Sai a zubar da ruwan

  3. 3

    Sannan,a kuma wankewa da ruwa mai kyau

  4. 4

    Sai a gyara kayan miya ajajjaga,adaka sauran kayan kamshin,shima daddawa adaka

  5. 5

    Sai a wanke ridin tas,adaka shima

  6. 6

    Sannan a zuba mangyada da kayan miya,a soya sama-sama

  7. 7

    A zuba sauran kayan kamshin,harda su daddawar,shima a soya sama-sama,a zuba magi da dan gishiri

  8. 8

    Sai a zuba ruwa daidai a tsaida sanwa.idan sanwar ya nuna kamar na mintoci ashirin,sai a zuba kayan cikin,hadi da nutmeg (yar miya)

  9. 9

    Sai kayan cikin na gab da nuna,sai azuba garin ridin,a jujjuya,sannan a rage wuta,abarshi su nuna na minti goma.

  10. 10

    Sannan a sauke.Aci lafiya

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Salwise's Kitchen
Salwise's Kitchen @cook_16516066
rannar
Zaria
I was born and bred up in Zaria
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes