Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Kaza
  2. Albasa
  3. Attaruhu
  4. Citta
  5. Gishiri
  6. Alayyahu
  7. Mai
  8. Kyan kamshi
  9. Maggi

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    A wanke kaza ayi mata yanka gida 4 sannan sai a samata gishiri a wanke ta atabbatar ta fita an fitar da duk dattin dayake jikinta, sai a juye a tukunya a zuba yankakkiyar albasa a raba lemon 🍋 tsami 2 a zuba a ciki

  2. 2

    Sannan a saka attaruhu shima a zuba akai, a goge danyar citta a zuba akai, sannan a saka curry, maggi, kyankamshi, citta, alayyahu

  3. 3

    Sai a zuba ruwa kadan a rufe sai a dora akan wuta a barta ta dahu so sai harta fara tafarfasa, sannan a bari ruwan ya kafe a jikin naman sai a sauke

  4. 4

    Sannan a sami karamar tabarya a dunga daddaka naman ya daku ba so sai ba, sannan ba a cire kashi a haka Zaki barta sai ki samu tray ki juye ki baza ya sha iska

  5. 5

    Sai a dora kaskon suya a wuta ayi amfani da me dan girma a zuba mai kadan saboda karyayi yawa a kawo albasa a zuba sai kisa ka naman ki Kiyi tajuyawa Har sai Kin gaya soyu

  6. 6

    Idan ya soyu sai ki sakashi a tray danyasha iska

  7. 7

    Aci dambun kaza lfy😋😋😋

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Mss_annerh_testy
Mss_annerh_testy @cook_16776895
rannar
Kano State

sharhai

Similar Recipes