Funkaso da Miyar Agushi da soyayyan naman kaza

Umma Sisinmama
Umma Sisinmama @cook_14224461
Kano

Funkaso da Miyar Agushi da soyayyan naman kaza

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki tankade fulawa ki zuba yeast da bakar hoda da gishiri ki jujjuya saiki saka ruwa ki kwaba da tauri saiki rufe ki saka acikin rana ko guri mai zafi.

  2. 2

    Zaki wanke kazar ki ki zuba a tukunya ki yanka albasa ki wanke ki zuba ki saka maggi da gishiri da kayan kamshi ki daura kan wuta inta dahu ki zuba mai a kasko ki daura akan wuta in yayi zafi ki zuba kazarki inta soyu ki juya daya barin inya soyu gaba daya ki kwashe.

  3. 3

    Saiki gyara kayan miyanki ki wanke ki nika saiki daura tukunya ki zuba mai in yayi zafi ki juye kayan miyan inya tafaso ki jika kanwa ki saka ruwan kadan kunfar ta fice saiki juye ruwan tafashen naman ki ki juya ki rufe suyita dahuwa.

  4. 4

    Saiki yanka alayyahun ki ki wanke da gishiri ki zuba a abin tace taliya saiki koma ki duba miyar ki in ruwan ya tsotse ki dan kara maggi kadan da gishiri dai2 yadda kikeso saiki dama agushin ki da ruwa yayi kauri kina diba kina tsumbulawa harki gama saiki rufe ki rage wutar bayan kamar minti biyar ki bude ki jujjuya saiki zuba alayyahun ki ki rufe yayi minti biyu saiki sauke miyar ki.

  5. 5

    Saiki daura kasko ki zuba mai ki saka albasa inya soyu ki kwashe ki dauko kwabin funkason ki zakiga ya kumburo saiki samu mara ki shafa mata mai ki debo kullin funkason ki saiki saka a bayan marar kidan faffada ki huda tsakiyar ki saka a mai haka zakiyi tayi harki gama inya soyu ki juya daya barin shima ya soyu saiki kwashe.

  6. 6

    Shikenan kin gama funkason ki da miyar agushi da soyayyen naman kaza.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Umma Sisinmama
Umma Sisinmama @cook_14224461
rannar
Kano
I was born in kano state
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes